Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Malam Muhammad Bello, ya kamu da COVID-19.
Da yake sanar da kamuwar tasa ranar Juma’a, Ministan ya ce amma tuni aka riga aka yi masa rigakafin cutar karo na daya da na biyu.
- An sake tsawaita wa’adin hada layukan waya da lambar NIN har zuwa karshen watan Maris
- Ban ji dadin yawan gyare-gyaren da Majalisa ta yi wa kasafin kudin 2022 ba – Buhari
Ya yi kira ga dukkan wadanda ba a yi musu rigakafin ba da su garzaya su je a yi musu saboda muhimmancinta.
“Bayan shafe tsawon wata 21 muna wasan buya da cutar COVID-19, daga karshe dai a wannan karon mun gamu a daidai lokacin da shekarar 2021 ke kokarin karewa.
“Bayan na jima ina jin rashin dadi a jikina tun daga 28 ga watan Disamba, na yanke shawarar na je a yi min gwajin.
“Sakamakon ya fito da safiyar Juma’a, kuma ya nuna ina dauke da cutar. Yanzu haka dai babu wasu manyan alamu, in ban da bushewar makogwaro da kuma mura da nake fama da su,” inji Muhammed Bello.
Ministan ya kuma jinjina wa ma’aikatan lafiya, musamman na Abuja, kan irin jajircewar da suke nunawa wajen yaki da cutar.
Kamuwar Ministan dai na zuwa ne kasa da mako daya bayan wasu hadiman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sun kamu da ita.
Daga bisani dai rahotanni sun ce mai magana da yawun Shugaban Kasar, Malam Garba Shehu, wanda shi ma ya kamu da ita, ya warke.