✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Minista ya taya Kabiru Yusuf murnar zama Shugaban kungiyar NPAN

Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya taya Shugaban Kamfanin Media Trust masu buga Jaridar Aminiya da Daily Trust, Kabiru Yusuf, murnar zama…

Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya taya Shugaban Kamfanin Media Trust masu buga Jaridar Aminiya da Daily Trust, Kabiru Yusuf, murnar zama Shugaban Kungiyar Masu Gidadjen Jarida ta Najeriya (NPAN).

Ministan ya aike da sakon taya murnar ne a wata ga hedikwatar kamfanin da ke Abuja a ranar Litinin.

Ya ce zaman Malam Kabiru zababben shugaban NPAN babbar nasara ce a bangaren harkokin gudanarwarsa a fannin aikin jarida.

“Ina alfahari da alakar da ke tsakanin ofishina da NPAN kuma ina fatan dorewar alakar ta kud-da-kud a zangon mulkinka.

“Na gamsu cewa, ta hanyar aiki tare ne kadai za mu iya tunkarar kalubalen da ke fuskantar kafafen watsa labarai a halin yanzu, musanman a wannan lokaci da ake fama da yaduwar labaran karya, kalaman batanci, wadanda hadarinsu ya bayyana a zahiri ga ingancin kafafen watsa labarai,” inji Lai Mohammed.

%d bloggers like this: