✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Minista ta bukaci matan Najeriya da su koyi sana’a

Ministar ma’aikatar kula da al’amuran matan Najeriya Aisha Abubakar, ta bukaci matan Najeriya da su yi koyi sana’o’in wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa kasar.…

Ministar ma’aikatar kula da al’amuran matan Najeriya Aisha Abubakar, ta bukaci matan Najeriya da su yi koyi sana’o’in wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa kasar.

Ministar ta bayyana hakan ne lokacin da Darakta Janar ta cibiyar ci gaban mata Misis Mary Ekpere-Eta tare da ayarin cibiyar suka ziyarce ta.

Hajiya Abubakar ta jinjina wa kokarin Darakta Janar ta cibiyar bisa kokarin da take yi na koyar da sana’o’i dabandaban  wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasar.