✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Minista a Daular Larabawa ya goyi bayan Shugaban Faransa

Wani minista a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Anwar Gargash, ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yarda da matsayar Shugaban Faransa Emmanuel Macron cewa akwai…

Wani minista a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Anwar Gargash, ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yarda da matsayar Shugaban Faransa Emmanuel Macron cewa akwai bukatar Musulunci “ya tafi daidai” da tsarin zamantakewa ko al’ummar Yammacin Duniya.

Minista Gargash ya fadin hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar Jamus mai suna Die Welt a ranar Litinin ta makon jiya.

Kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da ake zanga-zanga a kasashen Musulmi kan kalaman Macron dangane da Musulunci, bayan Macron din ya zargi Musulmi da “wariya” ya kuma kare wani zanen batanci ga Annabi (SAW) da ya janyo takaddama a duniyar Musulmi.

“Ya kamata Musulmi su kasa kunnensu da kyau su saurari abin da Macron ya fada a jawabinsa.

“Baya son ya mayar da al’ummar Musulmi saniyar ware a Yammacin Duniya, kuma maganarsa tana kan gaba,” inji  ministan a Ma’aikatar Harkokin Wajen Daular Larabawa.

Ya ce Musulmi na bukatar “su saje da tsarin da ya fi na yanzu” a kasashen Yammacin Duniya.

“Faransa na da hakkin zakulo hanyoyin da za a cimma hakan ta yadda za a yaki tsaurin ra’ayi da kuma gidadanci,” inji shi.

Gargash ya yi watsi da zargin cewa Macron yana so ne ya mai da al’ummar Musulmin da ke zaune a Faransa saniyar ware.

’Yancin yin zane

Bayan fuskantar kaurace wa kayayyakin Faransa mafi tsanani da kasashen Musulmi suka yi, Macron ya sassauta harshensa inda ya ce ya fahimci irin zafin da al’ummar Musulmin suke ji game da zanen batancin.

“Na fahimci irin radadin da suke ji kuma ina martaba su,” kamar yadda ya bayyana a wata hira da ya yi da kafar talabijin ta Al Jazeera ranar Asabar.

“Amma lallai ne ku fahimci aiki na a halin yanzu, shi ne yin abu biyu,  in karfafa zaman lumana kuma in kare wadannan hakkokin.

“Kuma a kullum zan kare ’yancin fadar albarkacin baki da rubutu da tunani da ma zane na Faransawa,” inji shi.