✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miloniyan da ya ci gaba da rubuta jarrabawar shiga jami’a bayan ya fadi sau 25

Ya ce har yanzu bai debe tsammanin shiga jami'ar ba

Wani miloniya mai shekara 55 a kasar China da ke son shiga Jami’ar Gaokao, inda ya rubuta jarrabawar neman shiga jami’ar sau 25 a jere, har yanzu bai yanke tsammanin cim ma burinsa na cin jarrabawar shigar ta ba.

Mutumin mai suna Liang Shi, ya mallaki Kamfanin Kayayyakin Gini a Chengdu, babban birnin Lardin Sichuan a Kudu maso Yammacin China.

Yana da isassun kudi don yin duk abin da yake so, amma bai zabi shiga jami’ar ta barauniyar hanya ba don cika burinsa.

Ya ce tun yana matashi yake mafarkin shiga Jami’ar Sichuan, kuma har yanzu bai cim ma burinsa ba.

A lokacin da akasarin mutane suka fara tunanin yin ritaya, Liang Shi ya mayar da hankali ne kan yin karatu mai zurfi don jarrabawar shiga Jami’ar Gaokao a bana.

Wannan shi ne karo na 26 da ya rubuta jarrabawa karo, inda ya yake fatan shi ne na karshe.

“Na cika shekara 55, kuma har yanzu ina matashi. Ba ni da matsala wajen koyon tarihi da tarihin kasa kawo yanzu. Idan zan iya shiga makarantar da nake so, zan kai karshen Gaokao, tsawon lokaci ina son in tafi makaranta. In ba haka ba, zan ci gaba da rubuta jarrabawar har sai na cika burina,” inji Liang.

Tun a 1983 ne Liang yake yin jarrabawar neman shiga Jami’ar Gaokao, kuma sau 14 ne kawai tun daga lokacin bai samu damar yi ba, a lokacin bai yi aure ba, kuma bai kai shekara 25 ba.

Mafi girman makin da ya taba samu shi ne maki 400 daga cikin maki 750 da zai iya ba shi damar shiga jami’a a mataki na biyu, amma ba makarantar da yake mafarkinta kamar Jami’ar Sichuan.

“Ni kawai na dauki shakkun da mutane yi a matsayinkwarin gwiwa kuma ina amfani da sakamakon jarrabawata don tabbatar da cewa, ba daidai na rubuta ba,” inji Liang Shi, inda ya ce, tsananin sha’awarsa ta shiga makarantar da yake mafarki ya sa yake rubuta jarrabawar duk shekara.

Mutane da dama suna ganin jarrabawar neman shiga Jami’ar Gaokao a matsayin mafi wahalar jarrabawar shiga jami’a a duniya, inda miliyoyin dalibai suke fafatawa don samun gurbi a manyan jami’o’in China.

Yawancin iyaye sun yi imanin cewa, wannan jarrabawar guda daya na iya nuna makomar ’ya’yansu a nan gaba.