✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mikel Obi yana neman matar aure

Shahararren dan kwallon Chelsea na Ingila da kuma kungiyar Super Eagles ta Najeriya John Mikel Obi ya ce har yanzu ya rasa irin matar da…

Shahararren dan kwallon Chelsea na Ingila da kuma kungiyar Super Eagles ta Najeriya John Mikel Obi ya ce har yanzu ya rasa irin matar da zai aura.
A wata tattaunawa da ya yi da wata jarida mai suna The Boss a Ingila, dan kwallon ya ce kawo yanzu ya bar wa Allah zabi ne a kan irin matar da zai zabar masa don ya aura.
Ya ce dalilinsa na yin haka bai rasa nasaba da yadda yake tunanin duk matan da yake samartaka da su a yanzu ba don Allah suke son sa ba, sai don abin hannunsa.  Ya ce “na tabbata da yawa daga cikin matan da nake soyayya da su a yanzu ba don Allah suke so na ba, amma saboda dukiyar da na mallaka kuma hakan ce ta jefa ni cikin tunani yadda zan samu kalar macen da za ta so ni tsakaninta da Allah”.
dan kimanin shekara 28, Mikel Obi, a ranar Litinin da ta wuce ne budurwarsa mai suna Olga Diiyachenko da ke Rasha ta haifar masa ’yan biyu.
Sannan wasu rahotanni sun tabbatar Mikel din ya taba haihuwa sau biyu da wasu mata daan-daan da ba a ambata ba.
Kafar sadarwar Pulse.ng ce ta kalato wannan bayani a lokacin da dan kwallon yake hira da jaridar The Boss in da ya ce “sauran mutane ba su da matsala wajen zabar kalar matan da suke so su aura, musamman wadanda ba su da kudi, amma ga masu kudi irina abin akwai wahala, gaskiyar magana akwai wahala don haka na bar wa Allah zabi”.
A kwanakin baya ne dai kocin Super Eagles Sunday Oliseh ya ki gayyatar Mikel Obi a wasan da Najeriya ta yi da Suwazilan inda ya maye gurbinsa da Paul Onobi.  Kocin ya ce ya zabi Paul ne maimakon Obi saboda ya fi nuna kwazo.