Shahararren dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake buga wa kulob din Chelsea na Ingila wasa John Obi Mikel ya fara shirin canza sheka zuwa kulob din Inter Milan da ke Italiya.
dan kimanin shekara 27 ya koma cin benchi ne a karkashin horarwar koci Jose Mourinho na Chelsea a kakar wasa ta bana da hakan ta sa sau goma kacal ya yi wasa a gasar rukunin Premier ta bana daga cikin wasannin da kulob din ya yi.
Kamar yadda rahotanni suka nuna dan kwallon ya yanke shawarar canza sheka ne tun da ya lura kocin ba zai cigaba da amfani da shi a kan kari a kulob din Chelsea ba. Tuni jami’an kulob din Inter Milan suka fara yunkurin tuntubar mahukunta kulob din Chelsea a kan yiwuwar dauke dan kwallon kafin a fara kakar wasa mai zuwa.
Haka kuma kulob din na Milan ya fara yunkurin dauke dan kwallon baya a kulob din Manchester United Nemanja bidic kafin a fara kakar wasa mai zuwa.
Mikel Obi ya fara shirin komawa kulob din Inter Milan
Shahararren dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake buga wa kulob din Chelsea na Ingila wasa John Obi Mikel ya fara shirin canza sheka zuwa…