Fa’iza Muhammad wacce aka fi sani da Fa’iza Badawa, daya ce daga cikin mawaƙan Kannywood.
Ita ta yi waƙar fim ɗin Oga Abuja, ɗaya daga cikin finafinan da suka yi tashe, ya kuma fito da basirar mawaƙiyar.
Kasancewar ta yi aure, mutane sun ɗauka ta daina harkar waƙa baki ɗaya. Sai a hirarta da wakilinmu Ibrahim Musa Giginyu, Fa’iza ta ce ba haka ba ne.
Yaushe kika yi aure?
Na yi aure ne a ranar 8 watan Afrilun shekar 2017, kuma ina zaune lafiya da mijina da kuma haihuwa daay da Allah Ya bamu, kuma aure ne na so ada kauna da kuma kyakkyawar kulawa. Kuma yana taimaka min tare da goya min baya a abubuwan ada na ke yi.
Shin gaskiya ne cewa auren ne ya hana ki ci gaba da waka?
Ba gaskiya ba ne. Har yanzu ina yin waka, kuma duk wasu manya-manya da ke wannan sana’a sun san har yanzu ina yin waka saboda muna aiki tare.
Duk lokacin da suke bukatar aiki da ni, su kan kira ni ko kuma su kira mijina tare neman izininsa na mu yi aiki ko aika masa sako zuwa gare ni.
Mu mawaka a bayan fage muke, ba ganinmu ake yi ba, sai dai a ji muryoyinmu wanda da shi a ke gane mu, da kuma cewa, yawancinmu mawaka mata da zarar mun yi aure sai mu daina aiki, shi ya sa da yawa suka dauka nima na daina waka.
A lokuta na kan yi wa abokan aikina bayani cewa, ina nan, na kuma ci gaba da sana’ata ta waka a wannnan masana’antar tamu.
Shin ko yaya ki ke tafiyar da wannan sana’a a yanzu da kina matar aure?
Wani tsari na fito da shi la’akari da tsarin addinina da kuma kula da matsayina a inda na kan bukaci duk mai son in yi mi shi waka da ya je ya gama rubuta wakarsa, ya kuma gama shiririnsa da wurin daukar murya.
Idan ya yi hakan, sai in nemi a sa min ranata ni kadai da zan je in yi nawa baitukan ko kuma dora murya. Inda na gama sai su ci gaba da sauran wadanda za su yi da su.
Kuma ya kamata ka sani cewa, ba ni kadai ce na ke da aure ba, na kuma ke waka, domin muna da yawa a yanzu fiye da yadda ka ke tunani.
Ka ga da akwai Zuwairiya Isma’ila, da Murja Baba, da Naja’atu Ta’Annabi, da Maryam A Baba, da Jamila Sadi, da Zainab Diamond, da Sa’a Bocal, da kuma Sa’a Nazifi Asnanic. Da sauransu.
Wane kalubale ne kike fuskanta a matsayinki na mawakiya kuma matar aure?
Ni babu wata matsala da na ke fuskanta a matsayina na matar aure kuma mai sana’ar waƙa musamman ma a gidan mijina.
Domin akwai kyakkyawar fahimta tsakanina da shi, bayan so da kauna, ya na bani sharwari tare da tallafa min a duk al’amurana ciki har da wannan sana’a ta waka.