✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mijin Kamala Harris ya ajiye aikinsa don samun shiga gwamnatin Biden

Mijin zababbiyar Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka, Kamala Harris, ya ajiye aikinsa a wani Kamfanin Shari’a da nufin samun wuri a fadar gwamnati duk da cewa…

Mijin zababbiyar Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka, Kamala Harris, ya ajiye aikinsa a wani Kamfanin Shari’a da nufin samun wuri a fadar gwamnati duk da cewa a baya ya ce ba zai shiga siyasa ba.

Doug Emhoff wanda babban lauya ne zai bar kamfanin DLA Piper a sa’ilin da za a rantsar da Joe Biden a matsayin Shugaban Amurka a ranar 20 ga watan Janairun 2021.

A watan Agusta ne Mista Emhoff ya karbi hutun barin aiki daga DLA Piper yayin da matarsa Kamala ta yanki tikitin takarar mataimakiyar shugaban kasa.

Yanzu dai Mista Emhoff yana aiki tare da kwamitin karbar mulki na Biden domin kulla dangartakar da za ta samar masa gurbi a gwamnatinsa kamar yadda wani jami’i a kwamitin ya shaida wa kafar watsa labarai ta Fox News.

Mista Emhoff kwararren lauya ne da ya shekara 25 yana wakilci a gaban kotuna daban-daban musamman a jihar California da sauran sassan Amurka.

Zai kafa tarihin zama mijin mace ta farko da ta zama mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka.

A watan jiya ne ya shaida wa mujallar People cewa ba shi da burin zama daga cikin mashawartan mai dakinsa ko da ta yi nasara a zaben da aka gudanar a ranar 2 ga watan Nuwamba.

“Ni mijinta ne, kuma haka kadai ya wadatar; Tana zagaye da muhimman mutane masu ba ta shawara a siyasance.

“Ni abokin zamanta ne, ba ta da wani amini da ya zarce ni kuma ni mijinta ne.

“Saboda haka abin da zan ci gaba da kasancewa a kai ke nan domin ba ta goyon baya”, inji shi.

A shekarar 2013 ne Emhoff da Kamala suka yi haduwa ta farko, kuma bayan shekara daya suka yi aure a wani dan kwarya-kwaryan biki.

Suna zaune a wani gidansu da darajarsa ta kai Dala miliyan biyar a unguwar Brentwood da ke Jihar Los Angleles kuma suna da wasu kananan gidaje a birnin Washington da San Francisco.

%d bloggers like this: