✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biden ya taya Trump murnar lashe zaɓe

Zan tabbatar da miƙa mulki cikin sauƙi, kuma ina gayyatar Trump zuwa Fadar White House domin mu tattauna.

Shugaban Amurka Joe Biden ya taya Donald Trump murnar lashe zaɓe ta wayar tarho kamar yadda Fadar White House ta tabbatar.

Biden ya bayyana cewa zai tabbatar da ya miƙa mulki cikin sauƙi, ya kuma gayyaci Trump zuwa Fadar White House domin su tattauna.

Zai kuma yi jawabi ga ’yan ƙasar ranar Alhamis kan sakamakon zaɓen da kuma shirin miƙa mulki, cewar sanarwar.

Biden ya kuma yi wa Kamala murnar kammala yaƙin neman zaɓenta mai cike da tarihi.

Wannan zuwa ne bayan da ’yar takarar jam’iyyar Democrats, Kamala Harris, ta amince da shan kaye a zaɓen da aka gudanar a ranar Talata.

Kamala Harris wadda ita ce Mataimakiyar Shugaba Biden, ta kira Donald Trump a wayar tarho domin taya shi murnar lashe zaɓen shugaban ƙasa, a cewar rahoton kafar yaɗa labarai ta CBS.

A yayin kiran ne kum Kamala ta jaddada batun miƙa mulki cikin lumana, da kuma zama shugaba na kowa da kowa ga Amurkawa, kamar yadda wani mai taimaka mata ya faɗa wa CBS.

Ana sa ran za ta yi wa jama’a jawabi a farfajiyar Jami’ar Howard a yau Laraba.

Kazalika, ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Trump ta fitar da sanarwa bayan Kamala Harris ta yi magana da shi inda ta amince da shan kayen.

Steven Cheung, darektan sadarwa na yaƙin neman zaɓen, ya ce Trump ya jinjina wa “jarumtar Harris, ƙwarewa, da jajircewa a lokacin yaƙin neman zaɓe da kuma bayansa, kuma shugabannin biyu sun amince kan muhimmancin haɗa kan kasar.”