’Yar takarar jam’iyyar Democrats, Kamala Harris, ta amince da shan kaye a Zaɓen Shugaban Amurka da aka gudanar a ranar Talata.
Kamala Harris wadda ita ce Mataimakiyar Shugaban Amurka, ta kira Donald Trump a wayar tarho domin taya shi murnar lashe zaɓen shugaban ƙasa, a cewar rahoton kafar yaɗa labarai ta CBS.
- Shugabannin duniya na ci gaba da aika wa Trump saƙon taya murna
- Mahara sun yi wa manoma 10 kisan-gilla a Neja
Yayin kiran, Kamala ta jaddada batun miƙa mulki cikin lumana, da kuma zama shugaba na kowa da kowa ga Amurkawa, kamar yadda wani mai taimaka mata ya faɗa wa CBS.
Ana sa ran za ta yi wa jama’a jawabi a farfajiyar Jami’ar Howard a yau Laraba.
Kazalika, ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Trump ta fitar da sanarwa bayan Kamala Harris ta yi magana da shi inda ta amince da shan kayen.
Steven Cheung, darektan sadarwa na yaƙin neman zaɓen, ya ce Trump ya jinjina wa “jarumtar Harris, ƙwarewa, da jajircewa a lokacin yaƙin neman zaɓe da kuma bayansa, kuma shugabannin biyu sun amince kan muhimmancin haɗa kan kasar.”