✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Miji ya tsere bayan Matarsa ta haifi ’Yan hudu

Wani magidanci a birnin Benin na Jihar Edo, ya cika bujensa da iska bayan da ya samu labarin cewa matarsa ta haifi ’yan hudu rigis…

Wani magidanci a birnin Benin na Jihar Edo, ya cika bujensa da iska bayan da ya samu labarin cewa matarsa ta haifi ’yan hudu rigis a lokaci guda.

Matar mutumin mai suna Rita Ndibisu ta haifi ’ya’ya hudu ne a wani babban Asibiti da ke kan titin Sakponba a birnin Benin a ranar 2 ga watan Janairun 2021.

Rahoto ya sanar cewa matar tana da wasu ’ya’yan biyar kafin zuwan wannan haihuwa ta ’yan hudu, wanda bayan samun wannan karuwa a yanzu tana da ’ya’ya tara kenan.

A halin yanzu mai jegon da ’ya’yanta na cikin koshin lafiya sai dai ana zargin mahaifinsu ya yi layar zana saboda gudun daukar nauyin dawainiyarsu.

Sai dai duba da yanayi na yadda rayuwar yanzu ta kasance, matar tana neman taimakon al’umma na gari da suka kawo mata dauki na tallafin abin da kula da yaran nata.