✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda neman aron kudi ya yi ajalin matar aure

Ya yi mata dukan kawo wuka saboda ya nemi aron kudi a wurinta ya rasa.

Wani magidanci ya lakada wa matarsa dukan kawo wuka har ta mutu saboda ta ki ba shi aron N2,000.

Mutumin da ke zaune da matarsa da ’ya’yansu uku a yankin Uselu a birnin Benin, Jihar Edo, ya dinga jibgar matar tasa, kafin daga bisa rai ya yi halinsa .

Babban dan ma’auratan, mai shekara 13 ya shaida wa manema labarai cewa, “Mahaifinmu ya dawo gida da misalin karfe 9 na dare, sai ya nemi mahaifiyarmu ta ba shi aron kudi N2,000.

“Da ta nuna masa babu kudin, nan take ya hasala ya fara fadar bakaken maganganu cewar tana tozarta shi a duk lokacin da ya zo neman aron kudi wajenta.

“Lamarin ya kai ga ya yi mata dukan tsiya har ta fara rashin lafiya; Na yi kokarin ba ta magani amma ya zubar da maganin.

“Bayan makwabta sun shigo sai aka dauke ta zuwa asibiti, a can ne aka tabbatar da mutuwarta,” a cewar dan.

Yaron ya kuma bayyana cewa mahaifin nasu na dawowa gida cikin maye wanda a sanadin hakan yake huce haushinsa a kan mahaifiyarsu.

Wasu daga cikin makwabtan magidancin sun nuna damuwarsu a bisa halin rashin dattakonsa, yadda yake dukan matar tasa kusan a kullum.

Kakakin ’yan sandan Jihar Edo, SP Bello Kontongs, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai yi karin bayani ba.