Kocin wucin gadi kuma tsohon kyaftin din Manchester United, Michael Carrick, ya bar kungiyar bayan shekara 15 a matsayin dan wasa da mai horar da ’yan wasa.
Carrick ya jagoranci kungiyar a wasan da ta doke Arsenal da ci uku da biyu.
- Najeriya A Yau: Yadda Mata Manoma Za Su Tsere Wa Maza A Bauchi
- Talauci zai kassaramu idan aka raba Najeriya — Osinbajo
A shekarar 2006 ce tsohon kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya dauko Carrick daga kungiyar Tottenham, sannan Mourinho ya rike shi a matsayin mataimakinsa bayan ritaya daga taka leda a shekarar 2018.
Ya karbi ragamar kungiyar ce bayan an sallami Ole Gunnar Solskjaer, inda ya buga wasa uku, ya ci biyu, ya yi kunnen doki daya.
Magoya bayan kungiyar sun yi zaton zai cigaba da kasancewa tare da sabon kocin riko da aka kawo, inda wasu ma suke cewa da shi aka bar ma rikon har zuwa karshen kakar bana a ga kamun ludayinsa musamman ganin ya fara da kafar dama.
Daraktan Wasanni na kungiyar, John Murtough, ne ya fitar da sanarwar cewa, “Michael Carrick ya bar Manchester United bayan shekara 15. Duk da cewa ba mu so ya tafi ba, amma mun amince da shawarar da ya yanke kuma muna masa fatan alheri.”
Da yake jawabi, Michael Carrick ya ce shi ne ya yanke shawarar barin kungiyar domin ya huta, “Ya kamata na yi ritaya da kwallon kafa in samu hutu, amma ban yi ba.”
A karshe ya ce zai ci gaba da kasancewa mai goyon bayan Manchester United.