Shahararren dan kwallon Ajantina da kulob din FC Barcelona na Sifen Lionel Messi yana murmurewa daga raunin da ya samu tun a watan Satumbar wannan shekara kamar yadda kocinsa na Barcelona Luis Enrikue ya sanar a ranar Talatar da ta wuce.
Sai dai kocin bai bayyana takamaiman ranar da Messin zai dawo filin daga a fagen kwallo ba. Amma ana kyautata zato zai dawo ne a ranar Asabar 21 ga watan nan da muke ciki watau ranar da kulob din FC Barcelona zai kece raini da na Real Madrid a gasar rukunin La-Liga na Sifen da ake wa lakabi da El-Classico.
A karshen makon jiya ne wasu jaridun da ake wallafa su a Sifen suka yada jita-jitar cewa da wuya dan kwallon ya murmure kafin wasan Real Madrid da na FC Barcelona a ranar 21 ga wannan wata da muke ciki.
Masana harkar kwallo na ganin kocin Barcelona Luis Enrikue ya ce Messi ya kusa dawowa ne don ya sanyaya zukatan magoya bayan kulob din da suka zaku da ganin Messi ya warke kafin wasan kulob din da na Real Madrid a wannan wata.
Kawo yanzu ’yan kwallon Barcelona Neymar da Luis Suarez ne suke haskakawa a kulob din tun bayan da Messi ya ji ciwo.