✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya share tarihin da Pele ya kafa a kwallon kafa

A karawar da kungiyar Barcelona ta yi da Valladolid a wasan gasar La Liga ranar Talata, fittacen dan wasanta, Lionel Andres Messi, ya zura wa…

A karawar da kungiyar Barcelona ta yi da Valladolid a wasan gasar La Liga ranar Talata, fittacen dan wasanta, Lionel Andres Messi, ya zura wa kungiyar kwallonsa cikon ta 644 yayin da Valladolid ta sha kashi da ci uku da nema.  

Hakan na nufin Messi ya kafa sabon tarihi a duniyar kwallon kafa ta kungiyoyi, inda ya zarce tsohon tauraron kwallon kafa na Brazil, Pele, wanda ya rike kambun tarihi na zura kwallaye 643 a kungiyarsa ta Sao Paulo.

Messi mai shekaru 33 a duniya, a yanzu ya buga wa kungiyarsa ta Barcelona wasanni 749 inda ya zura kwallaye 644.

Tarihi ya nuna cewa babu dan kwallon kafa da ya taba zira wa kungiya daya tilo kwallaye masu yawan wanda Messi ya ci wa Barcelona a yayin da a yanzu ya shafe rayuwarsa ta sana’ar kwallon kafa gaba daya a kungiyar.

Bayan tsallaka wannan mataki, Messi ya bayyana cewa bai taba tsammanin a rayuwarsa zai iya zarce tarihin da wani dan wasa makamancin Pele ya kafa ba.

Tun a karawar da Barcelona ta yi da kungiyar Valencia a wasansu na gasar La Liga da aka tashi kunnen doki a karshen makon da ya gabata, Messi ya yi kan-kan-kan da Pele da kwallaye 643 bayan ya taimaka wa kungiyarsa an tashi wasan biyu-da-biyu.

Daga kai wa wannan mataki, tsohon dan wasa Pele ya taya Messi murna tare jinjina masa dangane da zarrar da ya ke ci gaba da yi a fagen sana’arsa.