Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi, ya sake kafa wani sabon tarin zira kwallaye a gasar La Liga da ake bugawa a Sifaniya.
Zakakurin dan wasan ya kafa wannan tarihi ne a yayin da Barcelona ta lallasa Huesca ci hudu da daya a ranar Litinin da daddare.
- Yadda Mata Ke Neman Kawo Karshen Kashe-Kashe a Zangon Kataf
- An sace daliba kwana biyu kafin bikinta a Kano
- Sojoji sun aika ’yan Boko Haram 41 lahira a Borno
Dan wasan gaban ya zira kwallo daya a daya daga cikin rukunai biyu na wasan, wanda a sanadiyar haka ya zama dan wasan daya tilo a tarihi da ya jefa kwallaye 20 a kakar wasanni 13 a jere da suka gabata.
Antoine Griemann da Oscar Mingueza sune suka zira wa Barcelona ragowar kwallaye biyu a minti da 35 da kuma 53 na wasan wanda ya mayar da kungiyar ta koma harin matsayin Atletico Madrid take samar teburin La Liga da doriyar maki hudu.
Kazalika, wasan cikon na 767 da Messi ya buga wa kungiyar, wanda a haka ya cimma yawan wasannin da tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar, Xavi Hernandez ya buga wa kungiyar a tsawon lokacin da ya shafe tare da ita.
Haka kuma, kwallo ta biyu da Messi ya jefa a minti na 90 a wasan, ita ce cikon kwallo ta 660 da ya zira, wanda da haka ya sake zarta dan wasa mai biye da shi mafi zira kwallaye a tarihin kungiyar kungiyar Cesar Rodriguez da kwallaye 428.