Wanda ya fi zura wa Barcelona kwallo a tahiri Lionel Messi, ya koma filin karbar horo na kungiyar, bayan dambarwar da ta barke tsakaninsa da ita na yinkurin barin ta da ya yi.
Wannan shi ne karon farko da Messi zai yi atisaye da abokan wasansa a Barcelona a karkashin sabon mai horar da kungiyar Ronald Koeman.
Barcelona za ta fara wasanta na farko a kakar wasa ta bana ranar 27 ga watan Satumba.
Messi ya ki halartar filin atisayen tun lokacin da ya aike wa kungiyar sakon bukatar ficewa daga cikinta sannan ya kaurace wa gwajin cutar coronavirus da ake yi wa duk dan wasa kafin fara karbar horo.
Shugaban gasar La Liga ta Sifaniya, Javier Tebas, ya ce bai taba daukar cewa Messi zai bar Sifen ba.
“Muna son Messi ya kasance tare da mu a nan Sifen. Shi ne dan wasan da ya fi kowa a duniya a harkar kwallo don haka muna son ya kammala wasan sa a nan” inji Tebas.
Yana tare da mu shekara 20 muna so ya kasance tare da mu ba tare da ya koma wata gasar ba”, Inji shi.