✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya kafa tarihi a Inter Miami

Lionel Messi ya ci kwallaye goma a gasar Leagues Cup da ya buga wa Inter Miami.

Kyaftin din tawagar Argentina, Lionel Messi, ya kafa wani sabon tarihi a sabuwar kungiyarsa ta Inter Miami da ke Amurka.

Wannan dai na zuwa yayin da Inter Miami da Lionel Messi suka lashe Kofin Leagues Cup ranar Asabar bayan sun doke Nashville da ci 10-9 a bugun fenareti.

Wannan ne karon farko da kungiyar ta lashe kofin bayan ta dauki Lionel Messi daga kungiyar Paris Saint Germain ta Faransa.

Inter Miami dai ta yi nasara a kan Nashville ne yayin da gumurzu ya kai su zuwa bugun fenareti bayan wasan ya tashi da ci 1-1.

Messi ne ya zura kwallon farko a minti na 24 da soma wasa amma Fafa Picault ya farke wa Nashville bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Bayan Leonardo Campana ya kasa yin amfani da damarsu ta karshe, an tafi bugun fenareti wanda ya kai ga har gololi biyu sun buga fenareti – amma golan Inter Miami Drake Callender ya kade kwallon da takwaransa na Nashville Elliot Panicco ya cilla masa.

Lionel Messi ya ci kwallaye goma a gasar Leagues Cup da ya buga wa Inter Miami, lamarin da ya ba shi damar zama dan wasa mafi zira kwallaye a gasar.

Haka kuma, Messi ne ya lashe kyautar dan wasa mafi bajinta a gasar ta Leagues Cup.

Tsohon dan wasan Barcelona, wanda ya lashe kyautar ballon d’or sau bakwai, ya zura kwallo a duka wasanni bakwai da ya buga wa Miami tun da ya soma murza leda a kungiyar.