PSG ta soma tattaunawa da wakilan Lionel Messi bayan raba gari da ya yi da Barcelona a ranar Alhamis.
Bayanai sun ce bangarorin biyu sun yi tattaunawar farko a ranar Alhamis kuma a ranar Asabar suka ci gaba da ganawa domin amincewa da kwangilar da za ta kai ga Messi ya koma Faransa a kwangilar shekara biyu.
- Akwai mutum 9,000 masu cutar COVID-19 a Najeriya
- Daya daga cikin daliban Chibok ta tsere daga hannun Boko Haram
A kan haka ne Messi ya bayyana aniyar sa ta komawa PSG yayin da ake ci gaba da tattaunawa domin amincewa da kwangilar shekaru 2.
Kafar yada labarai ta Le Parisien ta ruwaito cewa tuni PSG da Messi sun cimma yarjejeniyar shekara biyu a tsakaninsu.
Idan har Messi ya koma Paris, zai rika karbar albashin Euro miliyan 40 kusan fam miliyan 34 a duk shekara.
Barcelona dai ta sanar da cewar ba za ta iya mutunta yarjejeniyar da ta kulla da Messi ba saboda rashin kudi da kuma dokar kula da gasar La Liga da ta kayyade irin kudaden da ya dace kowacce kungiya ta kashe, abinda ya kawo karshen zaman sa na shekaru sama da 20 a kungiyar.
Shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce ci gaba da rike Messi a kungiyar su zai haifarwa kungiyar asarar da zata kai na shekaru 50 saboda dokar gudanar da wasan kasar.
Barcelona ta ce yau Lahadi dan wasan na Argentina mai shekara 34 zai halarci taron ganawa da manema labarai inda zai bayyana a hukumance karshen zamansa na shekara 21 a Barca cikin mutunci.