Ana iya cewa tun bayan komawar Lionel Messi kungiyar wasa ta Paris Saint-Germain (PSG) koma-bayan da ya samu ta kai makura a makon da ya wuce inda Real Madrid ta tisa keyarsu gida daga Gasar Zakarun Turai.
Lamarin ya kai ga har magoya bayan PSG suna wa Messi, wanda sau bakwai yana lashe kyautar Ballon d’Or ihu ana tsaka da wasa ranar Lahadi. Shin kwalliya ta biya kudin sabunta?
Ga kadan daga cikin abubuwan bajinta da kuma koma-bayan da shahararren dan wasan dan asalin kasar Ajantina ya samu, tun bayan da ya bar Barcelona zuwa PSG.
– Bajintar Messi a PSG
Kwallon farko a ragar Man City
Bayan komawarsa PSG, Lionel Messi ne dan wasan da ya ci mata kwallon farko a babban wasansu na farko a kakar wasar, wanda suka fafata da Manchester City.
Duk da cewa kafin nan sai da aka buga wasanni uku ba tare da ya zura ko kwallo daya ba, amma kuma a gwabzawar tasu da Man City a Parc des Princes ranar 28 ga Satumba, 2021, shi ne ya ci Man City kwallon farko.
Leipzig: Cire wa PSG kitse a wuta
Bajintar Messi ta sake bayyana a Gasar Zakarun Turai duk da cewa an yi saurin cire su.
Sau tari sai an kusa cire kungiyar, dan wasan yake ceto ta, kamar a wasansu a gidan RB Leipzig a matakin rukuni.
Messi ya ci kwallaye biyu cikin minti bakwai da rabi, ciki har da kwallon da ya zura da daga gurbin buga fanareti, wanda da shi PSG ta samu nasara da ci 3-2 a kan masu masaukin baki.
Taimakawa a ci kwallo 3
Lokacin da Messi ya fara komawa PSG, ba a yi zaton zai yi wani tasiri wajen taimakawa a zura kwallaye uku a ragar kungiyar Saint-Etienne da ke neman gurbi a Gasar Ligue 1 ba.
Amma tauraron dan wasan ya haska a daren 28 ga Nuwamba, 2021, a wasansu da Saint-Etienne, wanda ya sa yanzu yake cikin wadanda suka fi taimakawa a ciki kwallo a gasar Faransa, 10 shi da Mbappe.
– An sha gaban Messi –
Lattin cin kwallon farko a gasa
Messi ya kasa cin kwallonsa na farko a PSG sai a watan Nuwamba, a wasansu da suka lallasa Nantes da ci 3-1. Kafin nan, ya kasa cin kwallo a karawarsu da Reims, Lyon, Rennes Rennes, Marseille da kuma Lille.
Rennes ta ba su kashi
Messi ya yi, ya yi, ammma ya kasa cin kwallo a farko-farkon kakar wasa bayan komawarsa PSG, inda Rennes ta ci su 2-0.
A wasan da aka fafata ranar 3 ga Oktoba, 2021, kocin PSG, Mauricio Pochettino ya fara wasan da Messi da sauran manyan ’yan wasansa – Mbappe, Neymar da kuma Angel Di Maria – amma ta duk da haka ba su ci ko kwallo ba.
Cire su a gasar cin kofi
A ranar 31 ga Oktoba Nice ta cire PSG masu rike da Kofin Gasar Faransa, wasan ne kuma Messi ya fara bugawa bayan warkewarsa daga COVID-19.
Bayan an sake yin canjaras babu ci a wasansu na biyu, golan da Nice ta aro daga PSG, Marcin Bulka, ya kama wa Nice kwallo a bugun fanareti.
Barar da fanareti
A ranar 15 ga Fabrairu, 2022, Messi ya shiga bakin duniya bayan ya barar da bugun fanareti a wasansu da Real Madrid inda golan Real Madrid Thibaut Courtois ya kade kwallon a minti na 62.
Ko da yake a karshe an tashi 1-0, bayan Mbappe ya ci Real Madrid daya mai ban haushi.
Waje-rod a Gasar Zakarun Turai
PSG da Messi sun sha mamakin gaske a Santiago Bernabeu ranar 9 ga Maris 2022, inda Real Madrid ta farke kwallaye biyun. Cikin kusan rabin lokacin da ya rage a tashi da wasan Real Madrid, Karim Benzema, ya karya alkadarin PSG, suka lallasa ta, tare da kora ta gida yadda Barcelona ta yi musu a 2017 da kuma Manchester United a 2019.
An yi wa Messi ihu
A ranar 13 ga Maris, magoya bayan PSG sun bayyana fushinsu da Messi kan abin da Real Madrid ta yi musu.
’Yan kallon sun dora laifin kayen da kungiyar ta sha a kan Messi da Neymar inda suka rika yi musu ihu, duk da cewa sun ci kwallo 3-0 a kan Bordeaux a ranar Lahadin a Parc des Princes.