✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mece ce makomar Gwamnonin G5?

Gwamna Makinde ne kadai ya kai bantensa a cikin gwamnonin G5.

Tun bayan zaben fidda-gwani na takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, da Alhaji Atiku Abubakar ya doke Gwamnan Jihar Ribas, Mista Nyesom Wike aka fara samun rikici a jam’iyyar.

Rikici ya kara zafi ne lokacin da Atiku ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Mista Ifeanyi Okowa ya mara masa baya, maimakon Wike, wanda ya ce Atiku da PDP sun yi masa alkawari.

Aminiya ta ruwaito yadda Jam’iyyar PDP ta shirya zaben gwaji domin zaben wanda zai mara wa Atiku, inda Wike ya zo na daya.

Wannan ya sa Wike da wasu gwamnoni biyar suka ware, suka fara yaki da takarar Atiku.

Gwamnonin na G5 sun gindaya wasu sharudda da dole a cika musu kafin su yi sulhu, su mara wa Atiku baya, daga ciki har da bukatar Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Iyorchia Ayu ya sauka.

Hakan ya ki samuwa har lokacin zaben Shugaban Kasa da aka yi ba tare da goyon bayan gwamnonin ba.

Gwamnonin su ne Nyesom Wike na Jihar Ribas da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Okezie Ikpeazu na Abiya da Samuel Ortom na Binuwai da kuma Seyi Makinde na Oyo.

Aminiya ta gano cewa, Atiku Abubakar ya fadi a jihohin gwamnonin biyar a zaben Shugaban Kasa.

Dan takarar Labour, Peter Obi ne ya lashe zabe a jihohin Enugu da Abiya, inda Bola Tinubu ya lashe sauran uku, wato Oyo da Binuwai da Ribas.

Daga cikin gwamnonin biyar, Ortom da Ikpeazu da Ugwuanyi da Wike duk sun kammala wa’adinsu na biyu, sai Makinde ne kawai ya nemi tazarce.

Yaya makomar gwamnonin da kokarinsu a zaben?

Ikpeazu

Gwamnan Abiya, Okezie Ikpeazu ya yi takarar sanata ne, sannan ya tsayar da Okey Ahiwe domin takarar Gwamnan da zai maye gurbinsa.

Gwamna Ikpeazu ya sha kaye a takarar Sanatan Abiya ta Kudu, inda dan takarar Jam’iyyar APGA, Enyinnaya Abaribe ya doke shi.

Gwamnan ya samu kuri’a dubu 28 da 422, shi kuma Abaribe ya samu kuri’a dubu 49 da 693.

Haka kuma dan takararsa na Gwamna, Okey Ahiwe ya da fadi inda dan takarar LP, Alex Otti ya samu nasara a kansa.

A karshe dai INEC ta ce Otti ne ya lashe zaben inda ya samu yawan kuri’u 175,467 da aka kada masa, yayin da ya sha gaban abokin karawar sa, Chief Okey Ahiwe na PDP, wanda ya samu kuri’u 88,529 da aka kada masa.

A Abiya ta Tsakiya, Jam’iyyar Labour ce ta samu nasara a zaben sanata, inda dan takararta, Darlington Nwokocha ya doke dan takarar PDP, Kanar Austin Akobundu (mai ritaya), sannan a Abiya ta Arewa Sanata Orji Kalu na APC ya lashe.

Wike

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike bai yi takarar komai ba, amma dan takararsa na Gwamna, Sim Fubara ya yi nasara a PDP, inda ya samu kuri’a dubu 302 da 614, dan takarar APC, Tonye Cole ya samu kuri’a dubu 95 da 274.

Haka ’yan takarar sanata da ya tsayar, ciki har da mataimakiyarsa ne suka lashe zaben sanatoci uku na jihar.

Wannan ya sa Wike yake cewa, “Zaben ya nuna kowa a fili. Na kawo Gwamna da sanatoci uku da ’yan Majalisar Wakilai mafi yawa da dukkan ’yan majalisar jiha.

“Ayu bai kawo komai ba. Shi ma Babangida Aliyu bai kawo komai. Don haka waye ya ci amana? Muna nan a PDP. Wannan ya sa muka ce a yi abin da ya dace suka ki.”

Ugwuanyi

Shi ma Ugwuanyi ya sha kasa a takarar sanata da ya yi a Enugu ta Arewa, inda dan takarar LP, Okechukwu Ezea ya doke shi.

Okechukwu Ezea ya samu kuri’a dubu 104 da 948, shi kuma Ugwuanyi ya samu kuri’a dubu 46 da 948.

Tuni dai INEC ta ayyana dan takarar gwamnan na Jam’iyyar PDP a Enugu, Peter Mbah, a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gudana a jihar ranar Asabar 18 ga wannan wata na Maris.

INEC ta ce Mbah ya cinye zaben ne bayan da ya samu kuri’u 160,895. Dan takarar Jam’iyyar Labour, Chijioke Edeoga, shi ne ya zo na biyu da kuri’u 157,552, yayin da Uche Nnaji na Jam’iyyar APC ya zo na uku da kuri’u 14,575.

Ortom

Shi ma Gwamna Ortom ya yi takarar Sanatan Binuwai ta Kudu, inda ya sha kaye a hannun dan takarar APC, Titus Zam.

Titus Zam ya samu kuri’a dubu 143 da 151, Ortom ya samu dubu 106 da 882.

Haka a zaben Gwamna, dan takarar APC, Rabaran Hyacinth Alia ya lashe zaben da kuri’a dubu 473 da 933 dan takarar PDP, Titus Uba ya samu kuri’a dubu 223 da 913.

Makinde

A cikinsu, Makinde na Jihar Oyo ne kadai ya sake tsayawa takarar Gwamna, wanda a lokacin ake tunanin ya yi kuskure. Sai dai zaben ya zo masa da sauki, inda ya samu kuri’a dubu 563 da 756 ya kayar da dan takarar APC, Teslim Folarin wanda ya samu kuri’a dubu 256 da 685.

PDP ta sauya Ayu

A yanzu dai kusan za a ce hakar gwamnonin ta cimma ruwa bayan da Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP ya amince da nadin Ambasada Umar Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban riko na jam’iyyar na kasa.

Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar bayan ganawar gaggawa da kwamitin gudanarwar PDP na kasa ya yi ranar Talata, ta ce ta dauki matakin ne don yin biyayya ga hukuncin Babbar Kotun Jihar Binuwai.

A ranar Litinin ne kotu a Binuwai ta haramta wa Ayu ci gaba da gabatar da kansa a matsayin shugaban PDP, har sai ta saurari karar da wasu ’ya’yan jam’iyyar suka shigar gabanta.

Da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron a shalkwatar PDP ta kasa, sakataren yada labaran jam’iyyar ya ce sun dauki matakin nada Damagum ne domin bin umarnin tsarin mulkin PDP.