✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mece ce makomar babban taron jam’iyyar APC?

A yau Lahadi ce Shugaba Muhammadu Buhari zai gana da gwamnonin jam’iyyar APC domin tsayar da ranar gudanar da babban taron jam’iyyar inda za a…

A yau Lahadi ce Shugaba Muhammadu Buhari zai gana da gwamnonin jam’iyyar APC domin tsayar da ranar gudanar da babban taron jam’iyyar inda za a zabi shugabanninta.

Wannan ganawa dai za ta gudana ne a yayin da jam’iyyar ke fatan ganin babban taron ya gudana a watan Fabrairu na gobe, la’akari da matsin lambar da take fuskanta daga Shugaba Buhari da ya bukaci ta warware duk wasu matsalolinta matukar ba ta son jam’iyyar adawa ta yi mata mahangurbar da za ta jawo mata rasa mulki a babban zaben kasa na 2023.

Sai dai wasu tun gabanin ya wakana, sun yi hangen cewa taron na ranar Lahadi ka iya zama tubalin assasa hadin kai ko kuma ya sake tarwatsa jam’iyyar.

‘Babu abin da zai hana mu gudanar da babban taron a watan Fabrairu’

Da yake ganawa da shugaban manema labarai na Fadar Shugaban bayan ganawar bayan labule da ya yi da shugaban kasar, Shugaban Kungiyar Gwamonin Arewa, Gwamna Simon Bako Lalung na Jihar Filato, ya ce taron na ranar Lahadi zai ta’allaka ne kan tsayar da ranar da za a gudanar da babban taron.

Gwamna Lalong ya ce gargadin da Buhari na cewa jam’iyyar ka iya rasa madafun iko ga jam’iyyar adawa ta PDP, alama ce da ke nuna muhimmancin jam’iyyar ta gudanar da taronta don gudun ka da ta wargaje.

A nan ne ya shaida wa manema labarai cewa a yanzu gwamoni sun bai wa shugaba Buhari tabbacin cewa taron zai gudana a watan Fabrairu.

A cewarsa, gargadin da Buhari ya yi ya nemi jam’iyyar ta rubanta kokarin domin aiwatar da abin da ya dace, yana mai cewa “kamar yadda sauran jam’iyyu suka gudanar da nasu babban taron, babu abin da zai hana mu gudanar da na mu.”

Sai dai Aminiya ta yi waiwaye kan dabdalar da ake ci gaba da shan fama da ita gabanin tsayar da wannan rana ta gudanar da babban taron jam’iyyar.

Tun a watan Nuwambar bara ne Shugaba Buhari ya amince da a gudanar da babban taron a watan Fabrairun bana.

Bayan wata ganawar sirri da ya yi shugaba Buhari a Fadar Aso Rock a ranar 22 ga watan Nuwambar 2021, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, ya ce Buhari ya amince da watan Fabrairu na 2022 a matsayin lokacin gudanar da babban taron jam’iyyar.

Duk wannan dai na zuwa ne yayin da tun da fari, jam’iyyar ta so gudanar da babban taron a watan Disambar bara, amma daga bisani ta sauya shawara saboda wadansu dalilai da ta bayyana.

A wata hirar da ya yi da BBC bayan ganawar sirri da suka yi tare da Shugaba Buhari, Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar, ya shaida cewar jam’iyyar ce ta yanke wannan shawara inda ta kuma tsayar da watan Fabrairu a matsayin lokacin gudanar da babban taron.

A cewarsa, “mun duba yiwuwar gudanar da wannan taro saboda a baya an sa shi karshen watan Disamba, wanda wannan lokaci ne da abokanmu gwamnonin jihohi Kudu da Kiristoci suke gudanar da shagulgulan bikin Kirsimeti, sai muka ga ya kamata a dage shi sai watan daya na badi.

“Sai muka ga cewa ko a watan dayan (Janairu), akwai zaben fid da gwani da Jihar Ekiti, aka ce to a kais hi watan biyu don a tabbatar da cewa an yi taro mai inganci.

“Da kuma aka tattauna aka wakilta mu je mu yi wa Shugaba Buhari bayani kan shawarar da muka yanke, sai Baba Buhari ya ce eh wannan tsari ya yi.”

Har yanzu ba a fara shirye-shiryen gudanar da taron ba

Duk da sanarwar da aka bayar a baya-bayan nan cewa za a kafa kwamitin kasafin kudi kan gudanar da babban taron, har yanzu babu wani abu da kwamitin rikon ya yi a kan wannan lamari.

Haka zalika, kwamitin rikon bai fara shirye-shiryen kafa kwamitocin shiyya-shiyya da za su tallata gudanar da taron ba.

Wannan tsaiko ya sa shakku ga kusoshin jam’iyyar da kuma masu neman mukamai daban-daban, domin har yanzu jam’iyyar ba ta tsayar da takamaimiyar ranar da za a gudanar da babban taron da aka shirya yi a watan goben ba.

Haka zalika Aminiya ta gano cewa, jam’iyyar ba ta yanke shawarar wurin da za ta gudanar da babban taron nata ba, wanda hakan ya sa ’ya’yan jam’iyyar cikin rudani.

Har ila yau, jam’iyyar ta yi gum a kan yaushe ne Kwamitin Amintattu zai gudanar da taronsa don tabbatar da jadawalin tsara babban taron.

Sai dai kwamitin da Gwamna Buni ke jagoranta ya sha bayyana cewa zai warware rigingimun da suke barazana ga jam’iyyar kafin shirya taron, domin samun hadin kai da samun nasarar gudanar da taron.

Akwai fargaba a tsakanin masu ruwa-da-tsaki cewa jinkirin gudanar da babban taron na iya shafar shiryeshiryen jam’iyyar a zaben badi, domin ana sa ran jam’iyyun siyasa su gabatar da jerin sunayen ’yan takarar zaben da za a yi a watan Fabrairun badi a watan Agustan bana.

Rikicin da ya biyo bayan taron jam’iyyar APC na jihohi

Wani abun takaici shi ne dambarwar da ta biyo bayan taron jam’iyyar APC na jihohi, inda a halin yanzu galibi akwai rikice-rikice da har ta kai ga wasu fustattun mambobin jam’iyyar sun shigar da korafe-korafe a gaban kotu, lamarin da ke barazana ga babban taron jam’iyyar na kasa da kuma kasancewarta a matsayin tsintsiya madauri daya.

Babu shakka taron da jam’iyyar ta gudanar na Mazabu, Kananan Hukumomi da kuma Jihohi ya kara dagula al’amura a wasu sassan jam’iyyar na jihohi wanda kuma ake ganin zai shafe ta a matakin kasa baki daya.

Bayan tarukan, ana samu rikici da ya mamaye wasu sassan jam’iyyar na jihohi, inda aka samu rikice-rikice a akalla jihohi 14 da suka hada da Legas, Bauchi, Imo, Enugu, Filato, Zamfara, Kwara, Gombe, Ogun, Osun, Oyo, Ekiti, Kano da kuma Taraba.

Alal misali, jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta fara fuskantar alkibar biyo bayan sulhun da aka yi tsakanin tsagin tsohon Gwamnan Jihar, Abdulaziz Yari da kuma na Sanata Kabiru Marafa.

Sai dai kuma sauyin shekar da gwamnan jihar, Muhammadu Bello Matawalle ya yi daga PDP zuwa APC ya kara dagula mata lissafi, inda kowane bangare yake hankoron kasancewa shi ne jigon da za a yi wa mubaya’a.

Fusatattun mambobin a Legas, Zamfara, Taraba, Ekiti, Kaduna, Kwara, Kano da kuma Kaduna, sun shigar da kara a gaban kotun yayin da kuma wasu suka yi barazanar yin hakan domin kalubalantar shugabannin jam’iyyar a matakin jiha da kuma tarayya.

Har ya zuwa, akwai korafe-korafe kimanin bakwai da ke gaban Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, wadanda suke kalubalantar sahihanci da kuma cancantar Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC na Kasa da ke karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Bunin a Jihar Yobe tun bayan kaddamarwar da aka yi wa kwamitin a ranar 25 ga watan Yunin 2020.

An nemi kotu ta dakatar da taron

Wasu ’yan jam’iyyar APC sun gurafanar da Kwamitin Riko na Jam’iyyar a gaban Babbar Kotun Abuja domin ta hana a gudanar da babban taron jam’iyyar.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, Suleiman Usman da Muhammad Shehu da Sama’ila Ashaka, da Idris Isah da Audu Emmanuel ne suke neman kotun ta dakatar da Kwamitin Rikon daga gudanar da taron a watan Fabrairu.

A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/3/2022, sun ce gudanar da taron a watan Fabrairu zai saba wa kundin tsarin dokokin APC.

Bayanai sun ce, masu korafin cikin karar da suka shigar mai kwanan watan 4 ga Janairun 2022, sun nemi a gurfanar da jam’iyyar APC, shugabanta da kuma Hukumar Zabe ta Kasa INEC.

Masu shigar da karar ta bakin lauyansu, Olusola Ojo, sun bukaci a dakatar da taron ne saboda a cewarsu, har yanzu wasu daga cikin tarukan a matakin jihohi ba su kammala ba.

Kawo yanzu dai kotun ba ta sanya ranar fara sauraron karar ba.

An nemi Buni ya ajiye aikinsa

Muryar Gwamnonin Kungiyar Gwamomin APC ta Progressive Governors’ Forum (PGF), ta yi kira ga Mai Mala Buni da ya ajie mukaminsa idan har ba zai kira babban taron jam’iyyar ba a watan Fabrairu.

Darakta Janar na PGF, Lukman Salihu ne ya yi wannan kira cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan ranar 5 ga Fabrairun 2022.

Rahotanni sun bayyana cewa Lukman Salihu ya yi babatu tare da bayyana fargabarsa kan makomar jam’iyyar.

A cewarsa, “jam’iyyar APC tana cikin tsaka mai wuya, kuma duk wani kokari na kara dage ranar gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa manuniya ce ta yadda ake wasarere da makomar jam’iyyar.

“Rade-radin da ke fitowa daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa Buni yana tafiyar hawainiya wajen kiran babban taron domin gwamnoni na son ganin sun ci gaba da jujjuya madafar ikon jam’iyyar a jihohinsu gwargwadon yadda suka ga dama.

“Akwai bukatar manyan jam’iyya su kira taron gaggawa domin a titsiye Buni da Sakataren Jam’iyyar na kasa, Johna Akpanudoedehe, domin gano dalilin wannan jan kafa da ake yi wajen gudanar da taron sannan kuma a samu masaniya kan barazanar da suke fuskanta,” inji Salihu.

Lukman Salihu ya kuma kalubalanci Buni da ya gabatar wa da Shugaba Buhari rajistar dukkanin ’ya’yan jam’iyyar.