A kwanakin nan, ana muhawara a shafukan sada zumunta a kan shin mene ne ‘Dannau’? Shin matsalar kwakwalwa ce ko kuma ta iska ce?
To, da ma an dade a duniya ana samun muhawarori iri-iri game da abubuwan da suke illata mu, su sabbaba mana cututtuka.
- Cutar Ebola ta sake bulla a Dimokuradiyyar Kongo
- Isra’ila ta rufe hanya daya tilo da Falasdinawa ke bi don shiga Zirin Gaza
Akwai su kuma da dama. Duk abubuwan da muke zama da su a duniyar nan wadanda muke gani da wadanda ba ma iya gani, wadanda muka sani da wadanda ma ba mu sani ba, za su iya illata mu.
Masu ilimin zamani mukan guji hada ilimomi wajen fayyace zance. Shi ya sa wasu lokuta za a ji muna cewa a likitance, saboda fassara ce kawai ta ilimin likitanci ba a hada da wani ilimi ba.
Amma idan za a shiga ilimin addinai a
shiga na zamani, a shiga na al’adu a kan mas’ala guda misali, za a iya samo bayanai gamsassu da dama.
Za a ga cewa shi ilimin addinai ya riga ya dasu, shi kuma na kimiyya da fasaha yanzu yake girma. Na al’adu kuma baya yake ci.
A wurinmu ma’aikatan lafiya, sanin wadannan ilimomin da aiki da kowane a inda ya dace zai iya taimaka mana wajen warware mana wasu mas’aloli da dama.
Shi ilimin addinai ya sanar da mu abubuwa da dama wadanda ko ilimin zamani bai sani ba, sai yanzu ne yake ‘gano’ wasu.
Ilimin likitancin zamani ilimin kimiyya
ne, ita kuma matsalar kimiyya ita ce aiki da zahiri da watsi da badini ko surkulle.
Don haka abin da ilimin kimiyya bai gani ba, ba zai sa shi a ma’auni ba. Kai qwayoyin cuta fa, tun shekaru aru-aru, ai ilimin addinai ya sanar da mu akwai su, amma ilimin kimiyya bai sa su a lissafi ba sai da aka fara ganinsu a madubin hangen kananan halittu.
Ke nan da za a kirkiro madubi mai ganin iskokai, likitancin zamani zai yi kokarin
danganta wasu matsalolin lafiya da sukan jawo.
Bari mu zo kan matsalar ‘Dannau.’ Ta fuskar ilimin addinai, malaman addinai sun yarda akwai shaidanu da kan danne mutane wadanda ba sa addu’o’i idan sun zo kwanciya barci, a danne mutum har ya kasa motsi.
Wai kada ka dauka ma a addinin Musulunci ne kawai, a’a har a addinin (Kirista mabiya) Katolika haka ne.
To wadannan bayanai na addini da alamun da akan ji idan hakan ta faru sai ya yi kama da bayanin likitanci a kan
sleep paralysis.
Wannan matsala ta sleep paralysis dadaddiyar matsala ce wadda tun kafin zuwan likitancin zamani akwai ta,
ballantana a ce ai yanzu aka gano ta.
To da yake likitancin zamani kamar yadda muka fada, yana so ne ya fayyace abin da yake zahiri kawai, sai ya gaza samun ainihin me za a alakanta wannan matsala da ita, sai aka alakanta ta da inda ake tunanin abin ke faruwa wato
kwakwalwa.
To dalilin ke nan da muke ganin likitancin zamani bai alakanta matsalar ‘Dannau’ da iska ba.
Amma kuma wannan ba yana nufin ko me ya taba kwakwalwar mutum a ce iska ba ne.