Ista rana ce da Kiristoci a fadin duniya suke tunawa da tashin Isah Almasihu daga matattu bayan an gicciye shi.
Kiristoci sun yi imani cewa Yesu Almasihu ya rasu a ranar Juma’a Mai Tsarki, sannan ya tashi daga matattu a rana ta uku, wato Lahadi, wadda ita ce ta zama ranar Ista.
- Fafaroma ya bukaci a tsagaita wuta a Ukraine
- Buhari ya gama lalata rayuwar ’yan Najeriya —Bishop Kukah
Wannan rana ta Ista tana da muhimmanci sosai a ruyuwar kowane Kirista, sobada imanin da suka yi cewa Yesu Almasihu, ya yi nasara da mutuwa domin fansar su daga zunubansu da na ’yan Adam baki daya.
Kiristoci sun yi amanna da cewa ranar da Yesu Almasihu ya tashi daga matattu, wato ranar Ista, ita ta ba kowane Kirista tabbacin samun cetonsa, wato rai na har abada bayan mutuwa.
Sun kuma yi imani da cewa Isa Almasihu ya dauke zunuban duk wanda ya gaskata da shi, shi ya suke farin cikin tunawa da wannan rana a kowace shekara.