Ya ku masu bibiyar Dausayin Kauna! A wannan karon mun shiga mako na uku a cikin wannan maudu’i, inda kuke ta warware bakin zaren wannan tukaddama dangane da dangantaka ko tarayya tsakanin jisuna biyu, mata da maza. Da fatan za mu ci gaba da bibiya.
Sako na farko ya zo ne daga Yusuf Suleiman Gusau, wanda ke cewa: “A gaskiya wani lokacin sai ka ga yarinya ta ce wa saurayi ba ta sonsa amma sai ya dage cewa lallai sai dai ita yake so ya aura. A karshe har ta kai da cewa wallahi idan aka daura masu aure sai ta kashe shi. Shi kuma yana daukar ai kawai barazana ce take yi masa, sai ka ga ya dage sai an yi auren. Daga karshe kuma idan da tsautsayi sai ka ga ta gabatar da aika-aikar da ta yi alkawari. Allah Ya kyauta.”
Yusha’u Kabir Ba’awa kuwa yana cewa: “Assalamu alaikum wa rahmatullah, FDK da fatan kana lafiya, yaya aiki? Zan tofa albarkacin bakina a kan al’amarin zamantakewar aure da soyayya. A tawa fahimtar, duk inda soyayya ta koma kiyayya to soyayyar ba ta ginu kan tubalin gaskiya ba, kuma duk matar da ta yi yunkurin hallaka mijinta ko nakasa shi, ina ganin hakan ba zai rasa nasaba da jahilci ba. A karshe muna addu’ar Allah Ya ganar da masu tunanin daukar irin wannan munanan matakai a masayin hanyar huce haushi gare su.”
Nasiru Kainuwa Hadeja (08100229688) da barkwanci ya bude tsokacinsa, inda yake cewa: “Matan Kano ga irinta nan! Anya ba ku kuka jawo Gwamnan Bauchi Bala Muhammad Kauran Bauchi ya tsallake matan Bauchi da na Kano ba? Karshe ma ya tsallake matan Najeriya gaba daya, ya haura ya auro Balarabiya. Ni kuma da hannuna da shuni, kafata zan wanke in nufi Indiya, in auro a can, tunda kun zama ababen tsoro.”
Wata da ba ta bayyana sunanta ba, ta rubuto cewa: “FDK, al’amarin ya wuce kima, akwai daurin kai. Mata na da nasu laifi, mazan ma da nasu, domin babu aminci kuma akwai son zuciya. Idan ba aminci a cikin aure, ka ga akwai babbar masala. Mata muna da son kai, ba mu son kishiya; don abin da wadansu mata suke dubawa shi ne gado, ba su son wata ta zo ta haihu. Ka ga hakan zai kawo babbar matsala. Su kuma maza ba su da hakuri, suna son mata da yawa kuma lokacin ana soyayya a yi ta dadin baki. ‘Ke kadai ce, ba zan kara ba.’ Ka gani, shi ya sa mata wani abu a rai, shi ne in an zo aure yake kawo matsala, sai ka dauka ma kamar ba su taba soyayya ba.”
Daga K. Bello Kiyawa (070-3252-8895): “FDK da sauran ma’abota bibiyar wannan fili mai tarin masoya, gaskiya ina ganin abin da yake kawo rikedewar soyayya zuwa kiyayya ba komai ba ne illa jahilci, rashin hakuri, rashin tsoron Allah, yaudara da karya da uwa uba kuma gina soyayyar ba don Allah ba.
In haka ne kuwa yana da kyau mu fara sanin mene ne so kuma mene ne kiyayya? In ya so sai mu san me ke jawo so ya rikide ya koma kiyayya?
Ko ban duba zuciyar kowa ba, na san duk lokacin da aka ambaci kalmar so, sai kowa ya tuna da wani ko wata da muka fi so a rayuwarmu (ba na nufin iya soyayya ta tsakanin saurayi da budurwa ko miji da mata), ina nufin so koma na mene ne. So dai wani halitta ne da Allah Ya jefa shi a cikin zukatanmu, yayin da muke jin wani irin shauki a duk lokacin da muka kamu da son wani ko wata har muke kyamar duk wani abu da zai cutar da abokan soyayyarmu, muke kuma iya yin duk wani abu da zai burge masoyanmu tare da nishadantar da su. Shi kuwa ki ko kiyyaya shi ne kishiyar so, ba su taba hada hanya ko ta ina domin kuwa duk lokacin da suka hadu to matsala ta faru ke nan.
Yanzu bari mu duba mu gani me ya kamata masoya su yi don guje wa fadawa tarkon kiyayya? Abin da ya kmata su yi tun farko dai shi ne:
1-Yin nazari a kan wanda ya cancanta a yi soyayya da shi. 2-Bai wa Allah zabin haduwa da masoyi nagari. 3-Kafa soyayyar domin Allah da sa tsoronSa a cikinta. 4-Yin hakuri da juriya ga wanda ake soyayya da shi, domin kuwa zo mu zauna zo mu saba ne. 5-Yarda da duk wata kaddara daga Ubangiji.
Bari in tsaya haka ba don na gama ba, sai don na ba wadansu wuri su ma su tofa albarkachin bakinsu. Allah Ya datar da mu, Ya hada mu da masoya nagari, Ya kuma sa mu fi karfin zukatanmu.”