✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ya sa malaman makaranta ke zanga-zanga a Iran?

Malaman sun sha alwashin ci gaba da gangami har zuwa ranar Alhamis

Malaman makaranta a biranen Iran fiye da 50 sun sha alwashin dorewa da zanga-zanga da yajin aikin da suka fara ranar Asabar, suna bukatar a kara musu albashi.

Jaridar Albawaba ta rawaito cewa malaman makarantar na bukatar karin albashin ne saboda su kubuta daga matsananciyar wahalar da matsin tattalin arziki yake haifar wa al’ummar kasar tun daga 2017.

Kamar yadda jaridar Iran International ta bayar da rahoto, malaman makarantar sun sha alwashin ci gaba da zanga-zangar ne har zuwa ranar Alhamis – ranar karshe ta mako a Iran.

Rahotanni sun ce zanga-zangar da aka yi a lardin Alborz da ke arewa da birnin Tehran ta fi kowacce tara jama’a.

‘Gidan kason malaman makaranta’

Kafofin yada labaran kasar kuma sun ambato kungiyoyin malaman makarantar, wadanda suka shirya zanga-zangar da yajin aiki, suna cewa jami’an tsaro sun yi dirar mikiya a kan gangamin da aka gudanar a garin Karaj, inda suka yi wa masu zanga-zanga duka suka kuma kama mutum 15.

Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sadarwa na zamani sun nuna yadda gungun masu zanga-zangar ke wakokin Allah-wadai da saba alkawarin da hukumomi suka yi, suna kuma kira da a saki wani malamin makaranta da aka garkame a gidan kaso.

“Daga Tehran zuwa Khorasan, malaman makaranta a gidan kaso suke”, inji su.

Wannan ne dai karo na shida a cikin wata uku da malaman na Iran ke shirya zanga-zanga.

Kuma kamar a lokutan baya, a wannan karon ma masu zanga-zangar sun yi tsinke wa ginin Majalisar Dokoki da ke Tehran da ofisoshin Ma’aikatar Ilimi a lardunan kasar.

Matsin tattalin arziki

Tattalin arzikin Iran ya fara fadawa cikin halin ni-’ya-su ne tun kafin barkewar annobar COVID-19, wadda ta kara dagula rayuwar ’yan kasar su kusan miliyan 84.

Tun bayan da tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya yi fancakali da yarjejeniyar takaita inganta makamashin nukiliyar Iran ya kuma kakaba mata sabon takunkumi, tattalin arzikin kasar yake ta fama da kalubale iri-iri.