A ranar Juma’ar da ta gabata ce Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan gwamnati, Abubakar Malami ya auri diyar Shugaban Kasa, Nana Hadiza Muhammadu Buhari, a wani aure da aka gudanar a ‘cikin sirri’.
Malami dai ya auri Hadizan ce a matsayin matarsa ta uku, kuma an daura auren ne a masallacin Fadar Shugaban Kasa bayan idar da Sallar Juma’a.
Sai dai bayanai na nuni da cewa an daura auren ne ba tare da an yayata shi ko an gayyaci mutane ko kafafen yada labarai ba.
Hatta hotunan daurin auren babu wanda ya gani, in ban da wasu na ma’auratan da suka dauka su biyu, da ke nuni da cewa sun zama mata da miji.
Tun da farko dai, duk yunkurin neman tabbatar da sahihancin labarin auren ma ya ci tura saboda babu wani tabbaci, in ban da jita-jitar da aka rika yadawa a kai.
‘Sam ba a yi biki ba, daurin aure kawai aka yi’
Sai dai wata majiya mai tushe ta tabbatar wa Aminiya cewa tabbas an daura auren ranar Juma’a, kodayake ba a yi kowanne irin biki ba.
Majiyar, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce, “Tabbas labarin gaskiya ne, yanzu ta tabbata Ministan Shari’a ya zama surukin Shugaban Kasa.
“Ya auri Hadiza, daya daga cikin ’ya’yan Shugaba Buhari ta wajen matarsa ta farko da ta rasu, Safinatu.
“An daura auren ne a masallacin Fadar Shugaban Kasa bayan idar da Sallar Juma’a, amma ba mutane da yawa a wajen.
“An shirya auren ya kasance cikin sirri ne, shi yasa hatta ’yan jarida ba a gayyace su ba,” inji majiyar.
‘Ba wannan ne aurenta na farko ba’
Wannan dai ba shi ne auren Hadiza na farko ba, domin a baya ta taba auren Abdulrahman Mamman Kurfi, amma daga bisani suka rabu.
Sai dai kafin rabuwarsu, bayanai sun nuna cewa sun haifi ’ya’ya shida tare.
Yanzu da wannan sabon auren, Hadiza ita ce za ta kasance matar Malami ta uku, saboda yana da mata biyu; Aisha a Fatima.