Mohammed Sani Jigirya wanda aka fi sani da Sallau na shirin Dadin Kowa mai dogon zango na gidan talabijin na Arewa 24, ya koka da yadda aka jingine shi daga shirin tsawon lokaci.
Fitaccen jarumin kuma mai wasan barkwanci ya shaida wa Aminiya cewa, rabonsa da ya fito a cikin shirin mai dogon zango ya kai shekara guda.
- Jami’ar Benin za ta fara bincike kan sarrafa makamin Nukiliya a Najeriya
- Najeriya na kan gaba wajen noma da shan Tabar Wiwi a duniya — NDLEA
Sallau ya kuma ce bai san dalilin da ya sa aka daina sa shi a cikin shirin ba.
Ya kuma ce, “Masu kallo na ta tambayata, ni kuma na rasa abin da zan ce mu su. Ban sani ba ko wani laifin na yi.”
Jarumin ya kuma koka da cire shi da aka yi daga wani dandalin WhatsApp na shirin, lamarin da ya sa hankalinsa ya tashi, ya kuma shiga neman mafita.
Aminiya ta tuntunbi Fauziyya D. Suleiman, daya daga cikin marubuta shirin, inda ta amsa da cewa, su da marubuta labari su ke aiki, ba da daidaikun ‘yan wasa ba.
“Duk wanda ba ka gani ba a Dadin Kowa, in dai har ba mutuwa ya yi a shirin ba, to yana nan watarana za a gan shi ya dawo,” in ji ta.
Shekara takwas ke nan da ake nuna shirin wasan kwaikwayon mai dogon zango a tashar ta Arewa24 a inda Jigirya ya ke fitowa a matsayin Sallau, wani mutumin karkara mai ban dariya, wanda da hakan ta sa ya yi suna.