✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MDD ta yi juyayin mutanen da Isra’ila ta kashe a Gaza

Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 11,000, yawancinsu kananan yara da mata da tsofaffi a Gaza.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kasa-kasa da tutocinta domin nuna juyayi kan mutanen da Isra’ila ta kashe a Zirin Gaza.

Ma’aikata sun yi shiru na kimanin minti daya a daukacin ofisoshin Majalisar Dinkin Duniyar a nahiyar Asiya a safiyar Litinin domin tunawa da mamatan.

Majalisar ta tuna da mutanen da aka kashen ne bayan da ta sanar da yawan mutanen da aka kashe a cibiyarta da ke Zirin Gaza.

Hukumar Jinkan Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya a (UNRWA) ta sanar a ranar Juma’a cewa an kashe jami’anta sama da 100 a Gaza, tun bayan fara yakin.

Isra’ila na ta yin luguden bama-bamai a fadin yankin Zirin Gaza tun bayan da mayakan Hamas suka kai mata wani kazamin hari a ranar 7 ga watan Oktoba, inda kungiyar ta kashe mutum 1,200 ta yi garkuwa da wasu 240.

Daga lokacin zuwa yanzu jiragen Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da 11,000, yawancinsu kananan yara da mata da tsofaffi a Gaza.