Kylian Mbappe ya nuna sha’awar tafiya Real Madrid ko Liverpool muddin ya bar kungiyarsa ta PSG. L’Equipe
Haka kuma Real Madrid ta soma shirye-shiryen samun damar daukar dan wasan mai shekara 22. AS
Mai horas da ’yan wasa a PSG, Mauricio Pochettino, ya ce kungiyar za ta bai wa Mbappe zabi a kan ra’ayin da yake ganin zai fisshe shi. Catalunya Radio
Tsohon Kocin Arsenal, Arsene Wenger, ya ce kungiyar ta yi sake damar daukar Mbappe kyauta ta subuce mata tun a lokacin da dan wasan yake Monaco. beIN Sport
Dan wasan Everton na kasar Colombia, James Rodriguez, ya fara duba yiwuwar barin kungiyar duk da yake a bazarar da ta wuce ya je kungiyar. Defensa Central.
Chelsea tana son dauko dan wasan Bayern Munich na kasar Jamus mai shekara 25, Niklas Sule. AZ
Kocin Kungiyar, Thomas Tuchel, yana sha’awar dauko dan wasan tsakiyar Borussia Monchengladbach na kasar Jamus, Jonas Hofmann mai shekara 28. Bild
Akwai yiwuwar Juventus za ta sake daukar dan wasan da sayar wa Everton a 2019 na kasar Italiya, Moise Kean, wanda ke a halin yanzu yake zaman aro a PSG. Le 10 Sport
Watakila Chelsea za ta bai wa AC Milan dan wasan Ingila mai shekara 23, Fikayo Tamori a mataki na dindindin, a yunkurin musayar dan wasan Ivrory Coast, Frank Kessi mai shekar 24. Il Milanista
Everton da Napoli na neman dauko dan wasan Real Madrid na kasar Sifaniya mai shekara 29, Lucas Vazquez. Todofichajes
Everton ta tuntubi Juventus kan dan wasanta na tsakiya, Adrian Rabiot, wanda ta yi masa farashin fam miliyan 30. Il Bianconero
Real Madrid tana son ta yi amfani da dan wasanta mai shekara 22 da ke zaman aro a Arsenal, domin janyo ra’ayin dan wasan Borussia Dortmund na kasar Norway, Erling Haaland mai shekara 20. Mundo Deportivo
Ana rade-radin Bournemouth za ta tabbatar da Thierry Henry a matsayin sabon kocinta a makon gobe. Mirror
Manchester City ta rage albashin da za ta rika biyan Lionel Messi idan ta dauko shi daga Barcelona. The Sun
A baya kungiyar ta kudiri aniyar biyan Messi fam miliyan 600 duk shekara a yunkurinta na neman kulla yarjejeniyar shekara biyar da dan wasan, amma yanzu ta zaftare albashin zuwa fam miliyan 430 saboda matsalolin da take fuskanta a karancin kudi.