Dan wasan gaba na kungiyar PSG Kylian Mbappe ya yanke shwarar ci gaba da zama a kungiyar bayan kwashe makonni ana danganta shi da tafiya kungiyar Real Madrid.
Jaridar wasannin kwallon kafa ta Goal.com ta ruwaito cewar Mbappe ya yanke shawarar ci gaba da zama a PSG da kuma rattaba hannu akan wani sabon kwantaragin shekaru 3 idan wa’adin kwantaraginsa na yanzu ta kare a ranar 30 ga watan Yuni mai zuwa.
- Rushewar gini ta kashe mutum biyu a Legas
- Batanci: ’Yan sanda sun soma bincike kan rikicin da ya barke a Bauchi
Wakilan Mbappe sun ki yin bayani akan sabuwar kwangilar da PSG za ta bashi, sai dai wasu rahotanni sun ce kungiyar za ta yi bayani dangane da yarjejeniyar da ta kulla da dan wasan na Faransa lokacin karawar da za suyi da kungiyar Metz a parc des Princes Yammacin ranar Asabar.
Batun sauya sheka ko kuma ci gaba da zaman Mbappe a kungiyar PSG ya dade yana daukar hankalin magoya bayan kungiyar da kuma na Real Madrid wadda ta lashi takobin daukarsa a karshen wannan kakar mai karewa.
Shi ma dan wasan bai taba boye sha’awar san komawa kungiyar Madrid ba, amma PSG ta yi iya bakin kokarinta wajen shawo kansa domin sake tunani har ya kai ga yanke shawarar ci gaban alakarsu.
Wannan matsayi ya nuna cewar Mbappe zai ci gaba da zama a PSG tare da Neymer da Lionel Messi domin taimaka wa kungiyar a yunkurinta na ganin ta lashe Kofin Zakarun Turai.
Jaridar Marca ta Spain ta ruwaito cewar Mbappe ya shaida wa shugaban Real Madrid Florentina Perez shawarar da ya yanke na ci gaba da zama a PSG.