✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mazauna gari sun kama ’yan fashi da makami biyu a Kano

Arcewar da magidancin ya yi ce ta ankarar da mutanen da ke wajen wadanda suka rufarwa ’yan ta’addan.

Mazauna yankin Yamadawa da ke Unguwar Dorayi Babba a Karamar Hukumar Gwale ta Jihar Kano, sun samu nasarar cafke wasu ’yan fashi da makami biyu yayin da suka kai wa wani magidanci hari da misalin karfe 11.00 na daren ranar Laraba.

Shaidu sun ce, lamarin ya faru ne da a cikin daren Laraba yayin da ababen zargin biyu suka yi kokarin yi wa wani magidanci fashi ta hanyar razana shi da bindiga yayin da yake kokarin shigar da motarsa gida.

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, arcewar da magidancin ya yi ce ta ankarar da mutanen da ke wajen wadanda suka rufarwa ’yan ta’addan har suka cimma su a yayin da suke kokarin tserewa a wani babur mai kafa uku.

Mutanen da suka yi dandazo wajen kama ’yan bindigar sun kuma mika su a hannun hukumar ’yan sanda da ke shiyyar.

A cewar wani shaidar gani da ido, sai da jami’an ’yan sandan suka garzaya da mutanen biyu zuwa asibiti saboda mummunar azabtarwa da mazaunan suka yi musu.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya inganta rahoton a ranar Alhamis.

Ya ce an samu bindiga da wuka a hannun ababen zargin da suka yi yunkurin kwacewa magidancin motarsa kirar Toyota Corolla.