✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mazauna Abuja Na Shan Ruwa A Kududdufi Ɗaya Da Shanu

Mata na fita neman ruwa tun ƙarfe huɗu na Asuba domin samo ruwan amfanin gida.

Al’ummar ƙauyen Shapi da ke yankin Kwali a Abuja sun roki Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya haƙa musu rijiya saboda wahalar ruwan da ya addabi yankin.

Jama’ar garin sun bayyana cewa suna ɗiban ruwa a kududdufi ɗaya da shanu musamman a lokacin rani irin yanzu.

Emma Yakubu, mazaunin Shapi ya kai wakilinmu wani kurman Kududdufi da ’yan garin ke ƙwaƙwalar ruwa domin sha da ayyukan yau da kullum.

Emma ya ce garin ya kai sama da shekara ɗari amma ba su da ko burtsatse ballantana rijiyar zamani.

Asabe Daniel, wata uwa a garin ta ce tana barin gidanta tun ƙarfe huɗu na Asuba domin tafiya wannan Kududdufin da a yanzu yake kandashe domin neman ruwan sha da amfani.

“Kullum idan ina buƙatar ruwa, ina barin gida tun ƙarfe huɗu na Asuba domin in samu wanda zan yi amfani da shi wurin sha da ayyukan cikin gida.”

Shugaban al’ummar yankin, Etsu Ishaku Ibrahim ya ce, “’yan siyasa sun san hanyar ƙauyen nan da ke da masu zaɓe sama da 400 lokacin kamfen, amma suna manta hanyar in sun ci zaɓe.”

Etsu ya kira ga Ministan Abuja da ya dubi wannan yankin nasu da idon rahama.

Wani da ke aiki a sashen ayyuka na hukumar yankin Kwali da bai so a ambaci sunansa ba, ya bayyana mana cewa an saka garin a cikin jerin garuruwan da za a yi wa burtsatse a wannan shekarar.