Hukumar Hisba a Jihar Kano ta koka kan yawaitar korafe-korafen yadda mazaje ke lakada wa matansu dukan tsiya a Jihar.
Kwamandan Hukumar, Shaikh Muhammad Ibn Sina, ya ce yanzu duka matan aure ya zama ruwan dare, inda a kullum ake kai wa hukumarsa irin wadannan korafe-korafe.
- Zamfarawa sun yi artabu da ’yan bindiga har maboyarsu
- Matar aure ta kashe budurwar da mijinta zai aura
- Zambar N12m ta sa an gurfanar da dan shekara 47 a gaban Kuliya
- Za mu gina Asibitoci 484 a kananan hukumomi 44 na Kano — Murtala Garo
Sheikh Ibn Sina ya bayyana damuwa kan yadda matsalar ta kai intaha a Jihar Kano, inda mazajen ke wuce gona da irin wajen lakada wa matansu dukan tsiya har su jikkata su.
“A kwanaki bakwai da suka gabata, mun karbi korafe-korafe har kashi 10 daga mata daban-daban wadanda mazajensu suka lakada wa duka wanda hakan ya nuna lamarin ya yi kamari,” inji Ibn Sina.
Kwamandan Hisban ya bayyana cewa hakan sabanin yadda ta kasance ne a lokutan baya ake samun korafe-korafen mata na daba wa mazajensu wuka a sassan jihar ne.
Ya ce amma a yanzu matsalar ta sauya fuska inda matan ke shan dukan tsiya a wurin mazajensu har ta kai sun raunatasu.
“Mafi alheri shi ne mutum ya zauna lafiya tare da iyalansa a madadin su bige da naushin juna,” inji Ibn Sina.
Ya hikaito ayoyi daga Al-Kur’ani mai girma da kuma koyarwar Annabi Muhammad (SAW) wadanda suka kwadwaitar da mazaje a kan nesantar kan dukan mata.