Tsohon dan damben boksin dan asalin Amurka Floyd Mayweather a ranar Litinin da ta wuce ya saya wa ’yarsa Iyanna mota kirar Marsandi samfurin AMG G63 da aka kera ta a bana (2019) kuma aka kiyasta kudinta a kan Fam dubu 150 (kimanin Naira miliyan 70).
Mayweather ne ya sanar da haka a shafin sadawarsa na Instagram inda ya ce ya yi haka ne saboda murnar bikin Kirsimeti.
Floyd Mayweather dai yana da dimbin tarihi a harkar damben boksin daga ciki har da wasa 50 da ya yi a jere ba tare da an doke shi ba, wanda hakan ya sa ya shiga kundin tarihi a bangaren damben boksin.