✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta yi garkuwa da daruruwan mutane

Sun yi ta kame mutanen garin ne ’yan kwanaki bayan dowawarsu gidajensu daga sansanin gudun hijira

Rahotanni sun bayyana cewa mayaka masu ikirarin jihadi na kungiyar ISIS a Yammacin Afrika (ISWAP), sun yi garkuwa da daruruwan mutane a Jihar Borno.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, mayakan a ranar Talata sun kai mamaya kauyen Kukawa da ke gabar Tabkin Chadi, inda suka rika yi wa mutane dauki dai-dai.

Harin ya auku ne a yayin da mazauna Kukawa suka dawo gidajensu bayan shafe shekaru biyu a sansanin ’yan gudun hijira na Babakura Kolo.

A watan Yunin da ya gabata, akalla sojoji 20 da fararen hula 40 sun rasa rayukansu yayin da daruruwan mutane suka jikkata a wasu tagwayen hari da mayakan suka kai a yankin.

Haka kuma a watan Yunin ne dai mayakan suka kashe akalla mutum 81 a wani mummunan hari da suka kai wani kauye a Karamar Hukumar Gubiyo ta Jihar Borno.