✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mayakan ISWAP sun yashe asibiti, sun kona turken sadarwa a Borno

Maharan sun kuma sace magunguna da kwayoyi a asibitin lokacin harin.

Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton mayakan kungiyar ISWAP ne a ranar Laraba sun kai hari asibiti sannan suka kona turken sadarwa a Karamar Hukumar Magumeri ta Jihar Borno.

Wani mazaunin yankin ya ce bayan sun mamaye hedkwatar Karamar Hukumar, sun rika harbi ta ko ina.

Wakilinmu ya gano cewa maharan sun kuma sace magunguna da kwayoyi a asibitin lokacin harin.

Kazalika, wani jami’in tsaro a yankin ya ce maharan sun kasa kansu gida biyu ne yayin harin.

Ya ce a daidai lokacin da sojoji suke musayar wuta da wasu daga cikinsu, ragowar kuma sai suka sulale zuwa asibitin inda suka dauke kwayoyi da firinji da kuma mayafai.

“Sun kawo harin garin ne ta baya, inda suka kona wani turken sadarwa, mallakin kamfanin Airtel, sannan suka yashe asibitin garin.

“Sun yi awon gaba da kwayoyi da firinji da kuma wasu mayafai,” inji majiyar.

Garin Magumeri dai na da nisan kimanin kilomita 40 daga Maiduguri, babban birnin Jihar ta Borno.