✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan ISWAP suka kashe mutun 14

Mayakan ISWAP, reshen kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga kungiyar ISIS (ISWAP), sun kashe mutum 14 a gabar Tabkin Chadi bayan mazauna sun dakile…

Mayakan ISWAP, reshen kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga kungiyar ISIS (ISWAP), sun kashe mutum 14 a gabar Tabkin Chadi bayan mazauna sun dakile isar abinci da sauran bukatu gare su.

Maharan sun yi aika-aikar ne a tsibirin Bulagaram ta bangaren Najeriya a yankin na Tabkin Chadi.

Kamfanin dillacin labarju na AFP ya ambato wata majiyar tsaro na cewa mayakan, “Sun far wa ganrin ne da misalin 6.30 na yamma yayin da ake shirin Sallar Maghriba, inda suka harbe shugabannin al’umma guda 14”.

Wata majiya kuma ta ce an harbe su ne a gidajensu, wasu kuma a masallaci, ko da yake ba a samu bambanci a adadin mamatan da suka fada ba.

A baya-bayan nan sarakunan yankunan sun yi taron sauke Al’kur’ani tare da tsinuwa ga duk wanda ya bari abuben bukata suka kai ga mayakan ISWAP.

Hakan ya fausta kungiyar da ke ganin matakin a matsayin juya musu baya da kuma goyon bayan gwamanti.

A makonnin baya hare-haren jiragen yaki na Najeriya a kan mafakar ISWAP sun halaka mayakanta da dama, kamar yadda AFP ta ruwaito.