✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan Houthi da Saudiyya sun tsagaita wuta a yakin Yemen

Bangarori biyun su dakatar da barin wuta albarkacin zuwan azumin watan Ramadana.

Bayan shafe tsawon shekaru ana gwabza yaki a Yemen ’yan tawayen Houthi sun cimma yarjejeniyar tsagaita buda wuta da kawancen sojin da kasar Saudiyya ke jagoranta.

Yarjejeniyar da aka cimma karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya za ta shafe tsawon watanni biyu ne a kasar da yaki ya daidaita, kana kuma tuni ta soma aiki ranar Asabar, daya ga watan Ramadana.

Bangarorin biyu da suka aminta da tsagaita buda wuta, sun kuma yi na’am da zirga-zirgar jirage daga wasu yankuna zuwa babban birnin kasar Yamen Sana’a, baya ga bude mashigar ruwa ta Hodeida da ke yammacin kasar ga tankokin dakon danyen mai, a cewar manzo na musamman na MDD da ya shiga tsakani, Hans Grundberg.

Tuni dai dakarun kawancen kasashen da Saudiyya ke jagoranta a yakin da suke yi da mayakan Houthi na kasar Yemen suka sanar da cewa za su tsagaita.

Matakin ya biyo bayan rokon da Majalisar Dinkin Duniya ta yi cewa bangarori biyun su dakatar da barin wuta albarkacin zuwan azumin watan Ramadana.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun dakarun kawancen Saudiyyar Turki al-Maliki ya fitar, ya ce za su yi duk mai yiwuwa wurin ganin tsagaita wutar da ake sa ran za ta fara aiki a ranar Asabar ta wannan mako ta yi nasara.

Sai dai a baya Gidan Rediyon Jamus ya rwuaito cewa tuni mayakan Houthi suka yi watsi da wannan tayi, inda suka ce babu wata tsagaita wuta mai ma’ana idan har kawancen na Saudiyya bai bude tashoshin jiragen ruwan kasar na Yemen ba.

A makon da ya gabata ne ’yan tawayen Houthi suka gabatar da tayin tsagaita wuta da tattaunawar zaman lafiya domin kawo karshen yakin da suka shafe shekaru kusan 7 suna gwabzawa da sojojin kawancen da Saudiya ke jagoranta.

Hakan dai na kunshe cikin wata sanarwa da wani babban jami’in Saudiyya ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Cikin tayin da suka gabatar, mayakan na Houthi sun yi alkawarin bude filin tashi da saukar jiragen sama na babban birnin Yemen, wato Sana’a, da kuma babbar tashar jiragen ruwa ta Hodeida.

Bukatar ‘yan Houthin na zuwa ne kwana guda bayan hare-haren da suka kaiwa sassan Saudiya da makamai masu linzami, ciki har da wata cibiyar mai a birnin Jeddah, lamarin da ya haifar da mummunar gobara da ta haifar da fargaba a tsakanin masu halartar gasar tseren motoci na Formula One.

Aminiya ta ruwaito cewa mummunar gobara ta tashi a wani rumbun ajiye mai na kasar Saudiyya da ke birnin Jeddah bayan ’yan tawayen Yemen na Houthi sun kaddamar da hare-hare a kasar.

Kafafen yada labaran Saudiyya a ranar Juma’a sun rawaito cewa hayaki ya tirnike sararin samaniya bayan da wasu makaman rokoki da ’yan tawayen suka harba suka fada kan rumbunan da ke birnin na Jeddah.

Ko da dai kafafen yada labaran Saudiyyar da ma kamfanin man kasar ma Aramco ba su ambaci sunan wajen ba, amma bayanai na nuni da cewa an kai harin ne a ma’ajiyar da aka taba kai wa harin a ’yan kwanakin baya.

Daga bisani dai da yammacin Juma’a, kakakin Houthi, Yahya Sarea, ya ce sun kai wa ma’ajiyoyin na Aramco hari ne da makamai masu linzami, yayin da suka kai wa matatun man da ke Ras Tanura da Rabigh hari da jirage marasa matuka.

Yahya ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma’a cewa, “Hare-haren an kai su ne a kan wuraren kamfanin Aramco da ke biranen abokar gabarmu [Saudiyya] na Jeddah da Riyadh

Ya kuma ce sun kai wasu hare-haren kan wasu wuraren na kamfanin na Aramco a  garuruwan Jizan da Najran da Ras Tanura da kuma Rabigh.

Hare-haren dai na zuwa ne yayin da Saudiyya take ci gaba da jagorantar kawancen da ke yaki da ’yan tawayen na Houthi, wadanda suka taba kwace iko da kasar Yemen a watan Satumban 2014.

Tun daga shekara ta 2015 ne dai mayakan Houthi da Iran ke goya wa baya a rikicin Yemen ke musayar wuta da kawancen Saudiyya da ke samun goyon bayan hukumomin Riyadh, lamarin da ya tilasta wa dubban mutanen Yemen kaurace wa gidajensu.