✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mayakan Boko Haram sun shiga kwana na 3 suna sheke ayarsu a Geidam

Akalla Mutum 11 ne ’yan gida daya aka tabbatar da kashe su sakamakon fashewar wani abu a garin.

Kwana uku kenan a jere mayakan kungiyar Boko Haram na cin karensu ba babbaka tun bayan kaddamar da hari a garin Geidam na jihar Yobe ranar Juma’a.

Sai dai ya zuwa yanzu Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni ya yi batan dabo, inda babu tabbacin ko yana jihar ko kuma yana Abuja inda galibi ya fi zama domin jagorancin jam’iyyar APC.

Mazauna garin na Geidam dai sun ce an rika musayar wuta tsakanin ’yan ta’addan da sojoji tun ranar ta Juma’a.

Sai dai bayan ruwan wuta daga sojojin sama wanda ya kori ’yan ta’addan, daga bisani sun sake dawowa garin suka ci gaba da ta’asa.

Akalla Mutum 11 ne ’yan gida daya aka tabbatar da kashe su sakamakon wani abin fashewa da ya tashi a unguwar Saminaka, kusa da sansanin sojoji na Geidam.

Wani mazaunin yankin, Abba Nura ya ce babu wanda zai iya tabbatar da ko sojoji ne ko kuma ’yan ta’addan ne suka tayar da bam din.

“Bayan mun shiga gidansu jim kadan da tsagaita wuta a harbe-harben, sai muka iske gawarwakin mutum 11 da suka mutu ba su sami agajin gaggawa ba,” inji Abba.

Sai dai ya ce saboda halin da ake ciki, ba zai yuwu a yi musu jana’iza a garin ba.

“Mun kai gawarwakinsu garuruwan dake da makwabtaka da Damaturu babban birnin jihar domin jana’iza. Duk mun rude, muna cikin tashin hankali, Allah ne kadai zai kawo mana dauki.

“Maganar da nake da kai yanzu, mutane sai barin garin suke, kuma ’yan ta’addan ba sa ce mana uffan in muna kokarin ficewa.”

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe, Dakta Mohammed Goje ya ce yanzu haka sun karbi wasu daga cikin mutanen garin kuma suna samin kulawa kamr yadda Gwamnan jihar ya ba da umarni.

%d bloggers like this: