Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne, sun kashe mutum 10 a garin Buni Gari da ke Karamar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, inda ‘yan ta’addan suka kashe wani mutum mai suna Abba Sheti Gawi mai shekara a duniya 40 lokacin da ya je saran itace a yankin Gangatilo.
- Gobe za a yi ta ta kare a Adamawa da Kebbi
- Gwamnati ta karrama limamin da ya tausasa kyanwa yana jan Sallah
Majiyar ta ce abokai da ‘yan uwan mamacin sun hada kansu domin bincike a yankin amma ‘yan ta’addar suka yi musu kwanton bauna.
“Ya zuwa yanzu idan aka hada da mutumin farko da suka kashe da wadannan da suka bi bayansa, za a ce sun kashe mutum 10 ke nan,” in ji majiyar.
“Mun ga sojoji da sauran jami’an tsaro za su je yankin domin kai daukin gaggawa,” a cewarsa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkareem, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ‘yan ta’addan mutum tara suka kashe.
A cewarsa, matasa tara ne suka rasa rayukansu bayan sun je neman dan uwansu da suke zargin Boko Haram sun yi awon gaba da shi.
Ya kara da cewa tawagar da DPO na yankin, DSP Idris Haruna ya jagoranta sun ziyarci wurin da aka kashe mutanen don gudanar da bincike.