✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mayakan Boko Haram sun kaddamar da hari a Damboa

Mazauna garin dai na zargin mayakan sun lalata turakun sadarwa.

Rahotanni daga garin Damboa na Jihar Borno sun ce yanzu haka mayakan kungiyar Boko Haram na can sun kaddamar da hari a Karamar Hukumar.

Wata majiya daga jami’an tsaro ta shaida wa Aminiya cewa ’yan ta’addan sun shiga garin ne da misalin karfe 5:00 na yammacin Asabar.

A cewar majiyar, jim kadan da kai mamayar mayakan a garin, hanyoyin sadarwa sun dauke, lamarin da ya sa ake zargin sun lalata turakun sadarwar garin.

Yanzu haka dai dakarun sojoji na can suna fafatawa da ’yan kungiyar ta Boko Haram.