A karon farko a tarihin wasan kwallon dawaki wato polo,kulob din Mad Air mallakar shahararren dan kasuwa Alhaji Lawal Dahiru Mangal ya shirya wasan sada zumunci a tsakanin ‘yan wasan dawakin da suka fito daga wasu sassa na kasar nan.
Kamar yadda Tim manajan kulob din na Mad Air Bello Buba ya shaidawa Aminiya a ranar da aka kammala wasan da aka yi kwanaki uku a filin wasan kwallon dawakin da aka fi sani da Gonar Dikko Ladan dake kan hanyar Jibiya ya ce sun yi tunanin shirya irin wannan wasa ne duk da ana cikin azumi don kara dankon zumunci a tsakanin ‘yan wasa.
Tim manajan ya ce, duk da ba kofi aka sanya a yayin gasar ba amma ya kara sa fahimta da kaunar juna a tsakanin ‘yan wasan da aka gayyato dag sassan kasar nan wadanda kuma matasa ne.
Ya ce alal misali an gayyato matasa ’yan kwallon dawaki irinsu Bashir Bashir da Khalifa wadanda suka fito daga Kano yayin da aka gayyato Musa da Shai’aibu danladi daga Bauchi. Sannan an gayyato Rabi’u da Usman Mohammad daga Kaduna yayin da aka gayyato Muhammadu Usman Sarki da shi kanshi mai tim din kuma mai masaukin baki Alhaji Lawal dahiru Mangal daga Jihar Katsina.
Shi dai wasan kwallon dawaki wanda marigayi Sarkin Katsina Dikko ne ya kawo sama da shekaru 100 da suka wuce ana yinsa ne a duk bayan shekara a kuma rukuni-rukuni inda ake yin gasar cin kofuna kuma a Jihar Katsina ne ake bude gasar kafin a yi a wasu sassan kasa.
A da, wasan ana kallonsa ne a tsakanin ‘ya’yan sarakuna ne amma daga baya ya samu karbuwa a tsakanin masu hannu da shuni da kuma matasa.
An dai kammala wasannin lafiya tare kuma da rarraba kyaututtuka ga wadanda suka buga wasannin.
Max Air ya shirya wasan kwallon dawaki
A karon farko a tarihin wasan kwallon dawaki wato polo,kulob din Mad Air mallakar shahararren dan kasuwa Alhaji Lawal Dahiru Mangal ya shirya wasan sada…