A Lahadin da ta gabata ce, fitaccen mawaki Nazir M. Ahmad; wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya angwance. Hakan shi ya kawo karshen rade-radin da jama’a suka jima suna yi na cewar zai auri fitacciyar jarumar fim din Hausa Hadiza Aliyu Gabon.
Kafin zuwan wannan rana, jama’a suna ta yada jita-jitar cewa mawakin zai auri Hadiza Gabon. Hakan ba zai rasa nasaba da yadda jama’a ke yawan ganin jarumar tare da mawakin ba. An dade ana yawan ganin su tare a lokuta daban-daban, musamman ma duk wani taro da shi mawakin zai gabatar ko zai je, akan yawaita ganin su tare.
Auren jarumin ya kawar da wannan jita-jita ta hanyar angwancewa tare da amaryarsa, Hadiza Isyaku Ahmad. An daura auren nasu ne a masallacin Murtala da misalin karfe sha daya da rabi na safiyar Lahadin da ta gabata.
Limamin masallacin Murtala, Sheikh Malam Kabiru dantaura ne ya jagoranci daurin auren a bisa sadakin Naira dubu arba’in. Wakilin ango, wanda kuma ya kasance yayansa, Misbahu M Ahmad ne ya mika sadakin.
Tun kafin ranar daurin auren, an gudanar da shagulgulan biki a wurare daban-daban da suka hada da otel din Royal Tropicana da kuma Country Mall, wadanda duk suke a birnin Kano.
Jim kadan da kammala shagalin, wakilinmu ya tuntubi ango, mawaki Nazir dangane da rade-radin da aka dade ana yi game soyayyarsa da Hadiza Aliyu Gabon. mawakin ya ce: “Babu wata soyayya tsakanina da ita sai dai akwai kyakykyawar alaka tsakaninm da ita. Hakan shi ne ya sa jama’a suke ganin kamar akwai soyayya a tsakaninmu da ita amma sam-sam ba haka ba ne.”
Taron bikin ya sami halartar mawaka da dama tare da jaruman fim din Hausa, wadanda suka hada har da ita Hadiza Aliyu Gabon.
Mawakin Hausa Nazir Ahmad ya angwance
A Lahadin da ta gabata ce, fitaccen mawaki Nazir M. Ahmad; wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya angwance. Hakan shi ya kawo karshen…