Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ja hankalin Musulman jihar a kan su ci gaba da koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (S.A.W).
Obaseki ya bayyana haka ne cikin jawabin taya murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam da ya ke gudana a ranar Alhamis.
- Maulidi: Gwamnati ta ba da hutu ranar Alhamis
- Maulidi na nuna karfin Musulunci ne – Sheikh Dahiru Bauchi
- Mauludi: Ganduje ya raba wa Malaman darika 110 shanu da shinkafa
Obaseki ya ce, “Ina taya Musulmai maza da mata na jihar Edo da ma kasa baki daya murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).
“A wannan rana muna kira da Musulmai mu ci gaba da nuna kauna da zaman lafiya, domin cigaban jiharmu da kasa baki daya”, inji shi.
Ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da zama makwabta nagari kamar yadda Ma’aikin ya koyar.
Daga nan sai ya yi kiran samun hadin kan mutanen jihar domin wanzuwar zaman lafiya.