An ceto wani makaho mai shekaru 65 a lokacin da yake ƙoƙarin faɗawa a cikin teku da nufin kashe kansa a Jihar Legas.
An ceto dattijon ne a kan Gadar 3rd Mainland, zai faɗa a cikin take, saboda rashin iya ɗaukar nauyin iyalinsa.
Dattijon ya tafi gadar ne tare da ’ya’yansa biyu maza masu shekaru 12 da kuma 16, wadanda ya umarce su da jefo shi a tekun.
Yaran suna ƙoƙarin jefa mahaifin nasu ne wani mutum ya hango su, aka ceto dattijon.
- Sojojin 196 sun ajiye aiki a Najeriya
- NAJERIYA A YAU: ‘Karin Farashin Mai Ya Fara Tilasta ‘Yan Najeriya Ajiye Aiki’
Da aka bincika abin da ke faruwa, sai makahon ya bayyana cewa ’ya’yansa ne kuma shi ne ya ba su umarnin yin hakan, saboda tsananin ƙuncin rayuwa da talauci da yake ciki.
Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce a ranar Alhamis aka ga mutumin da ’ya’yan nasa za su jefa shi a tekun, aka sanar da ’yan sanda.
“Mutumin ya bayyana cewa ya yanke shawarar halaka kansa ne saboda gwamnati ta riƙa kulawa da ’ya’yan nasa bayan rasuwarsa,” in ji Hundeyin.
A cewar jami’in, hukuma tana ƙoƙarin tuntubar matar makahon da kuma tallafa wa iyalan.