Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu, Bawan Allah Muhammad, tare da alayensa da sahabbansa baki daya da kuma duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, yau ma mukalar tamu, ci gaba ne kan sinadarai ko makaman da ake tunkude Shaidan da su wajen tabbatar da ikhlasi a cikin ayyukan ibada. Za mu tashi ne daga:
6. RASHIN TASIRANTUWA DA MAGANGANUN MUTANE: Mutumin da za a ce ya yi gam-da-katar (ya dace da daidai) shi ne wanda ba ya tasirantuwa da yabon mutane (wato ba ya jin an zuga shi) dangane da ayyukan da yake gudanarwa na ibada. Idan ma mutane suka yabe shi da alheri, wato suka yi na’am da abin da yake yi na da’a, wannan yabon ba zai kare shi da komai ba, sai ma kankan da kai da tsoron Allah; sai ma ya ji a jikinsa cewa yabon da mutanen suke yi masa, wata fitina ce a kansa, saboda haka sai ya roki Ubangijinsa Ya tserar da shi daga wannan fitina.
Babu wani da ake amfanuwa da yabonsa; ko a cutu da zarginsa, sai Allah kadai. Saboda haka sai ka mayar da mutane a matsayin wadanda ke cikin kabari (wadanda suka riga suka mutu aka sanya su cikin kabari), a matsayinsu na wadanda ba su jawo maka wani amfani ko tunkude maka wata cuta. Wato ta yadda, idan har wanda ke cikin kabari zai iya amfanar da kai da wani abu ko ya tunkude maka wata cuta, to, yabon mutane ma zai iya amfanar da kai ko zarginsu zai iya cutar da kai da wani abu a rayuwarka.
Ibn Aljauziy, (Allah Ya jikansa), a cikin littafinsa Saidil Khadir, a mujalladi na daya, shafi na 67, yana cewa, “Barin dubi zuwa ga abin halitta da tunkude wani ganin tagomashi daga zukatansu kan wani aiki da tsarkake nufi da boye abin da ake ciki, shi ne abin da ya daukaka matsayin wadanda aka daukaka, a tsakanin al’umma.”
Wato su masu matsayin daraja a addinin nan, sun samu wannan darajar ne don sun guje wa kambama ayyukansu na ibada, sun boye su matukar babu bukatar a bayyana su, kuma sun nisanci ganin mutane da yabonsu, sun nemi yabon Allah kadai, sun yi kokari wajen guje wa zarginSa, alhali ba ruwansu da zargin mutane ko yabonsu.
7. kUDURCE CEWA MUTANE BA SU MALLAKI ALJANNAH KO WUTA BA: Idan bawa ya kasance yana ji a jikinsa cewa wadanda ake yin riyar aikin ibada dominsu da sannu za su tsaya tare da shi a Ranar Tsayuwa (bayan an tayar da matattu domin yin hisabi), suna masu tsoro (a tsorace), alhali duk suna tsirara, sai ya farga cewa lallai sarayar da niyyar aikin ibada dominsu, ba muhallinta ba ne. Wato bai dace ya yi tunanin yana aikin ne dominsu, balle har ya ji zai samu wata karuwa ta yabo daga gare su ba.
Wannan al’amari tabbas ne, domin su wadancan mutane (da suke tsaye tare), ba za su iya rage masa radadi da wahalar da ake shiga cikinta ba a Ranar Hisabi, hasali ma dai suna cikin halin da yake ciki na kunci, a wannan ranar. Saboda haka, idan ka fahimci haka kuma ka kudurce shi a ranka, ka ji a jikinka, to ka san cewa lallai shi ikhlasi (tsarkake niyya don Allah) a aikin ibada, hakkinsa shi ne kada a sarayar da shi ga kowa, sai ga Wanda Ya mallaki Aljannah da wuta kadai.
Saboda haka ya zama wajibi ga mumini ya kasance mai yakini (gaskiyar tabbatar abu ba tare da ko sofane na akasin haka ba) cewa mutane ba su mallaki Aljannah ba, balle su gabatar da ita gare shi (su shigar da shi cikinta), kuma ba su da wani iko na fitar da shi daga wuta, ko da ya nemi su fitar da shi din. Kai, hasali ma in da duk mutane za su taru gaba-dayansu, tun daga na farko har zuwa na karshensu, suka tsaya bayansa suna mara masa, don su samu su fitar da shi, ba su iya samun iko yin haka, ko kuma su shigar da shi Aljannah ba za su iya ba ko daidai da taki daya. In kuwa haka abin yake (kuma lallai haka din yake), to, don me za ka rika yin riyar aikin ibadarka saboda mutane, ko kake waigawa gare su, alhali ba su mallaki komai ba, ko su mallaka maka wani abu?
Malam Ibnu Rajab, (Allah Ya jikansa), yana cewa a cikin littafinsa Jami’ul Ulumi wal Hikam, mujalladi na daya, shafi na 67, “Duk wanda ya yi azumi, ya yi Sallah, ya yi zikirin Allah, ya yi nufin samun abin duniya da haka, ba shi da wani alheri tare da shi a cikin duk wadannan; saboda babu wani amfani a cikin yin haka, ga mai aikin ibadar, musamman saboda abin da ya tattaru gare shi na laifi (sabo) shi kansa, ba a kan waninsa ba.” Wato aikin ba zai amfane shi ba, balle waninsa.
Sannan lallai wadanda kake kyautata (kawata) aikin ibadarka dominsu, saboda su yabe ka, bukatarka ba za ta samu biyuwa daga gare su ba, sai ma dai mai yiwuwa su zarge ka, kuma ka kaskanta a wurinsu, sai kuma kin ka ya yi naso a cikin zukatansu. Wanda tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi, yana cewa, “Wanda duk ya yi riya, Allah Zai sa a yi riya da shi.” Muslim ne ya ruwaito Hadisin. Wato Allah Zai bar shi da wadanda ya yi riyar saboda su don su yi masa sakamako.
To amma idan ka tsarkake aikin ibada don Allah, sai Allah Ya so ka, sai kuma sauran halittu su so ka. (Allah) Wanda tsarki ya tabbatar maSa Yana cewa, “Lallai wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka na kwarai, Mai rahama Zai sanya musu so.” Wato wanda ya bi Allah da gaskiya, Allah Zai sanya zukatan mutane su so shi, kamar yadda yake a cikin Hadisin da Imamu Tirmizi ya ruwaito daga Sa’ad da Abu Huraira (Tarjamar Ma’anonin Alkur’ani, shafi na 465).
8. TUNANIN KANA CIKIN kABARI TILONKA: Rai yana yin kyau, ya gyaru saboda tunani a kan makomarsa. Idan bawa ya hakkake a ransa cewa za a cusa shi a cikin kabari, shi kadai dinsa, ba tare da kowa ba, kuma ya yi yakinin ba wani abin da zai amfane shi ban da aikinsa na kwarai; kuma lallai dukkan mutanen duniya ba za su iya dauke masa komai ba na azabar kabari; sannan kuma dukkan al’amurra a Hannun Allah kadai suke; to a wannan lokaci ne bawa zai tabbatar da yakinin cewa babu abin da zai kubutar da shi, sai ikhlasin aikin ibada ga Wanda Ya halicce shi, Shi kadai, Mai girma da daukaka.
Za mu dakata a nan, sai mako na gaba, ina Allah Ya kai mu. Allah Ya taimake mu tsarkake ayyukan ibada dominSa Shi kadai, ta yadda za mu samu tsira!
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!!