✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsayin azumtar watan Ramadan a Musulunci (5)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna…

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Ya da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne (SAW).

Allah Ya dada tsira da aminci ga ManzonSa da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, kodayake yau mun kwarari kwana 23, duk da haka za mu gabatar da bayani ne kan I’itikafi, sannan sai Zakkar Fidda-Kai da Sallar Idi, duk a takaice. Amma kafin nan akwai bukatar mu kara tunatarwar a kara mayar da hankali wajen hasashen Lailatul kadri (Daren Daraja) a cikin wadannan kwanuka, saboda in an dace da shi, to, mutum zai samu lada kamar ya yi aikin ibada na fiye da shekara tamanin da kari. Allah Ya yi mana muwafaka.
Bayani kan I’itikafi: Ma’anar I’itikafi ita ce tsayuwa ko kebantuwar mutum kan yin wani abu, saboda haka wanda ya lizimci (ya like wa) masallaci, ya tsayu a cikinsa don ibada, alhali yana azumi – sai a ce shi mai I’itikafi ne, kamar yadda bayanin haka ya zo a littafi Almisbahul Munir, mujalladi na 2, shafi na 424 da kuma Lisanul Arab, mujalladi na 9, shafi na 252. Ba a yin I’itikafi a ko’ina sai a cikin masallaci, saboda abin da Alkur’ani ya fadi a surar Bakarah, aya ta 187 cewa: “… Kuma kada ku sadu da su (mata) alhalin kuna I’itikafi a cikin masallatai.”
Sannan kuma da abin da ya gudana na I’itikafin matan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), a cikin masallaci kuma cikin kunci. Da ya inganta a yi shi a gida, to, da sun aikata hakan ko da sau daya ne a rayuwarsu.
Jamhurun (mafi rinjayen) magabata sun tafi a kan cewa ana shar’anta yin I’itikafi a cikin kowane masallaci, sai dai sun yi sabani ne kan sharadin masallacin ya kasance na Juma’a ko waninsa. Wasu kuma suka ce ba a yin sa sai a masallatai uku na Harami (Makkah) da na Annabi a Madina da na kudus kadai, amma dai maganar farko ita ta fi rinjaya ga karbuwa.
Ana kwadaitar da yin I’itikafi ne a cikin watan Ramadan, saboda Hadisin da aka samu daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) da ya ce, “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya kasance yana I’itikafin kwanaki goma a cikin kowane watan Ramadan, amma a shekarar da ya rasu, ya yi kwana ashirin ne.” Buhari ya fitar da shi a Hadisi na 2,044. Annabi ya yi I’itikafi a goman karshe na watan Shawwal. (Buhari, 2,041 da Muslim, 1,173)
Mafi falalar lokacin yin I’itikafi shi ne cikin goman karshe na wata Ramadan, saboda abin da ya tabbata daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam), “Ya kasance yana I’itikafi a cikin kwanaki goman karshe na watan Ramadan, har zuwa lokacin da Allah Mabuwayi da daukaka, Ya karbi ransa.” Buhari ya fitar da shi a Hadisi na 2,026 da Muslim a Hadisi na 1,172.
Mata suna iya yin I’itikafi, idan an samu kyakkyawar dama ta kubuta daga aukuwar kowace irin fitina.
Ana shiga I’itikafi ne kafin magariba ko bayan an kammala Sallar Asuba, duk yadda aka yi, ya yi daidai. Daga nan sai a shagaltu da duk abin da yake na da’a ga Allah Ta’ala, kamar yin Sallah da tilawar Alkur’ani da zikirori da istigifari da addu’o’i da salati ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da sauran ayyuka.
I’itikafi yana baci idan mutum ya sadu da matarsa ko ya yi abin da ya fitar masa da maniyyi; ko in an fita daga masallaci ba tare da wata lalura da aka shar’anta ba, kamar cin abinci, yin ba-haya ko wanka ko alwalla, ko makamantan haka.
Zakkar Kono: Ana kiranta Zakkar Fidda-Kai, kuma ana fitar da ita ne kafin a fita zuwa Sallar Idi, idan watan Shawwal ya tsaya. Ana fitar da ita kwana daya ko biyu kafin ranar Sallah. Sunnah ce wajiba da Manzon Allah (SAW) ya wajabta a kan kowane Musulmi namiji da mace, da ko bawa, babba ko yaro, kowannensu mudunnabi hudu, wato sa’i daya ke nan na masara ko dawa ko gero ka shinkafa da makamantansu. Idan aka bayar da ita bayan Sallar Idi, ta zama sadaka kawai.
Abu Sa’idul Khudri (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Mun kasance muna fitar da Zakkah a zamanin Annabi (SAW) sa’i na abinci, kuma a lokacin abincinmu shi ne sha’ir da zabib da cukui da kuma dabino.” Buhari da Muslim sun ruwaito shi.
Mutum yana fitar wa duk wanda ciyar da shi yake kansa tun daga ’ya’ya har barorin gida, maza da mata, kowanensu sa’i daya.
Ana bayar da ita ga mabukata wato fakirai da miskinai don su ma su samu abin da za su ci a ranar Sallah saboda kada su yi bara, ta yadda kowa zai yi ta hada-hadar karewar azumin Ramadan.
Duk wadannan bayanai suna cikin Hadisan su Abdullahi bin Abbas da Abdullahi bin Umar (Allah Ya yarda da su), kamar yadda Buhari da Muslim da Abu Dauda suka ruwaito.
Hikimar fitar da zakkar kuwa ita ce don a tsarkake mai azumi daga yasasshiyar magana da batsa, a yayin azumin; sannan da ciyar da masu rauni.
Sheikh Usaimin, ya ce, “Daga hikimar Zakkar Fidda-Kai akwai kyautata wa masu rauni don tsare su daga roko da bara a ranar Idi, su ma su yi tarayya da masu hali wurin murna da farin ciki. Kuma da ita ake tsarkake mai azumi daga tawayar da ya samu sakamakon aikata wani laifi ko yasasshiyar magana a lokacin da yake azumi. Kuma bayyanar da farin ciki ce bisa ni’imar Allah ta kammala azumin Ramadan da sallolin da aka gudanar a cikin wannan wata mai albarka.”
Sallar Idi: Sallar Idi, Sunnah ce da ake yi ta raka’a biyu a filin Idi, ko cikin ginannen masallaci idan akwai lalura. Ana yin kabbara bakwai (7) a raka’ar farko tare da kabbarar harama, sannan a karanta Fatiha da sura; a raka’a ta biyu kuma za a yi kabbara biyar (5) ne tare da kabbarar tsayuwa, sannan a karanta Fatiha da sura. Mutum na iya yi shi kadai, in bai samu damar zuwa filin Idi ba.
Tun farko idan mutum zai fita zuwa filin Idi, ana son ya yi wanka na ibada, ya yi kwalliya da sabuwar sutura, in da hali; ya shafa turare, sannan ya fita yana kabarbari – Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!! Ko kuma ya rika cewa Allahu Akbar, Allahu Akbar, la’ilaha illallahu, Allahu Akbar, wallahu akbar, walillahil hamd – yana yi yana hutawa har ya isa filin, ya zauna ya jira liman, sannan a yi Sallah. Ba a nafila kafin ko bayan sallar. Ana son a yi kokarin gayar da juna da yi wa juna fatar alheri da ziyartar ’yan uwa da abokan arziki don taya su murnar kewayowar wannan rana!
Ina ganin nan za mu dakata, sai mako na gaba, in Allah Ya kai mu, mu yi magana a kan azumin nafila. Wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh!