Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta wa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne (SAW).
Allah Ya dada tsira da aminci ga ManzonSa da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, mun kwana bayan mun karanci wasu daga cikin abubuwan da ake kwadaitarwa a kansu game da azumtar Ramadan, yau za mu tashi ne daga:
Gargadi kan karya azumin ramadan da gangan:
Daga Abu Umamah Albahiiliy (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana cewa: “Wata rana ina barci, sai wadansu mutum biyu suka zo mini, suka kama ni ta wajen damatsana suka zo da ni wajen wani dutse mai ban mamaki, sai suka ce, ‘Hau kansa.’ Sai na ce, ‘Ba zan iya hawansa ba.’ Sai suka ce, ‘Za mu saukake maka shi.’ Sai na kama hawa, har sai da na kai kusan karshensa, sai na ji wasu saututtuka masu tsanani, sai na ce, ‘Wadanne irin saututtuka ne wadannan?’ Sai suka ce, ‘Wannan kururuwar mutanen wuta ne.’ Daga nan sai suka wuce da ni, har sai ga ni ga wadansu jama’a an sagale su a wuyoyinsu, ana yagar habobinsu jini na ta kwarara ta wurin, sai na ce, ‘Su wane ne wadannan?’ Suka ce, ‘Su ne wadanda suke bude-baki kafin azuminsu ya cika (ai manufa, kafin lokacin buda-bakin ya yi. Wato suna karya azumin da gangan)…” Annasa’iy ya ruwaito shi cikin littafin Alkubra – kamar yadda yake a littafin Tuhfatul Ashraaf, mujalladi na 4, Hadisi na166; da Ibnu Hibban (Lamba ta 1,800 a Zawa’idah); da Alhakim, mujalladi na 1, Hadisi na 430 ta hanyoyi masu yawa daga Abdurrahman bn Yazid Ibn Jabir daga Sulaim bn Amir, kuma isnadinsa ingantacce ne.
Kodayake Hadisin da yake cewa, “Wanda ya sha rana daya cikin Ramadan ba tare da wani uzuri ba (wato da gangan), ko don rashin lafiya ba, to, bai rama shi ba, ko da ya azumci shekara ne a madadinsa.” Buhari ya ‘allaka’ shi a cikin sahihinsa a mujalladi na 4, Hadisi na 160, a Fathul Bariy, ba tare da isnadi ba. Kuma Ibn Khuzaimah ya sadar da shi a cikin sahihinsa, Hadisi na 1,987 da Tirmiziy a cikin Kubra, kamar yadda ya zo a cikin Tuhfatul Ashraf, mujalladi na 10, Hadisi na 373; da Baihakiy, mujalladi na 4, Hadisi na 228; da Ibn Hajar a cikin Taghlikit Taghliki, mujalladi na 3, Hadisi na 170 ta hanyar Abu Almudawwis daga babansa daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi); Ibn Hajar ya ce a cikin Fathul Bariy, mujalladi na 4, Hadisi na 161, “An yi sabani mai yawa a cikinsa kan Habib bn Abu Sabit, ta yadda illoli uku suka auku a cikinsa: Akwai ‘iddirabi’ (kai-komo); ‘juhala’ (rashin sanin) halin Abu Almudawwis; da kuma ‘shakka’ kan ko mahaifinsa ya ji daga Abu Huraira.
Sannan Ibn Khuzaimah, bayan ya ruwaito Hadisin, sai ya ce, “In har ya inganta, to ni dai ban san Abu Almudawwis ba, balle babansa.”
Duk da wadannan bayanai, Hadisin mai rauni ne, ba a kafa hujja da shi, sai dai akwai bukatar mai aikata gangancin karya azumi a cikin watan Ramadan ya ji tsoron Allah, ya girmama hurumin watan, saboda irin muhimmancin matsayin da yake da shi a Musulunci, wanda shi ne kanun bayaninmu tun da muka fara wannan mukala.
Abubuwa wajibai da mai azumi zai nisanta:
Akwai bukatar ka sani, cewa shi mai azumi shi ne wanda dukkan gabbansa suka kame daga dukkan zunubai, kuma harshensa ya kame daga karya da alfasha da shaidar zur, kamar yadda ya zo a Hadisin Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam), ya ce, “Duk wanda bai bar zur da aiki da shi ba, to, Allah ba Ya da bukatar barin cinsa da shansa.” Buhari, mujalladi na 4, Hadisi na 99.
Lallai ne cikinsa kuma ya kame daga karbar abinci da na sha; farjinsa ya kame daga jima’i, harshe daga lagawu (yasassar magana, ko zagi ko abin da ya yi kama da haka), tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana. In zai yi magana, to, ba zai fadi abin da zai cutar da azuminsa ba; in kuma zai aikata wani aiki, to ba zai yi wanda zai bata masa azumin ba; saboda haka sai kalamin da zai fito daga bakinsa ya kasance mai kyau, mai dadi, kuma aikinsa ya zamo salihi, abin yabo.
Idan ya yi haka, sai a ce yana azumin da aka shar’anta masa, amma ba azumin kamewa daga ci da sha da sha’awa kadai ba. Saboda haka kamar yadda ci da sha da biyan bukatar sha’awa suke bata azumi, to, haka zunubai suke sukurkuce sakamakonsa, su bata ladarsa ta yadda zai koma kamar wanda ma bai yi shi ba.
Lallai Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam), ya kwadaita wa mai azumi ya sifantu da kyawawan dabi’u, ya nisanci alfasha da wuce wuri cikin kutsawa ga abubuwan da shari’a ba ta amince da su ba, a kowane lokaci ma, balle a cikin wata mai alfarma, kamar Ramadan.
Abin da yake halal ga mai azumi:
Babu laifi idan alfijir ya riski mutum cikin janaba (Buhari, mujalladi na 4, Hadisi na 123 da Muslim, Hadisi na 1,109). Ko kuma ya yi ta yin aswaki (amfani da itacen goge baki), a duk tsawon lokacin azumin (Buhari, mujalladi na 2, hadisi na 311 da Muslim, Hadisi na 252; Fathul Bari, mujalladi na 4, Hadisi na 158; Sahihu Ibn Khuzaimah, mujalladi na 3, Hadisi na 247; Sharh Assunnah, mujalladi na 6, Hadisi na 298.
Ko kurkurar baki da shaka ruwa, sai dai kuma akwai bukatar a yi kaffa-kaffa wajen yin hakan; ko hada jiki (wato runguma) da sumbatar matarka, kodayake matashi ya kamata ya yi sannu-sannu don kada ya fitar da maniyyi a yayin yin haka; ko yin kaho; ko dandana abinci; ko sanya kwalli da makamantansa; ko kwara ruwa a kai ko yin wanka don saukaka kishi da zafi; duk wadannan babu laifi don an aikata su, sai dai kuma akwai bukatar kiyayewa.
Waiwaye:
Kodayake yau muna rana ta 16 ga wata, akwai bukatar a tuna wa mai azumi muhimmancin yin sahur da jinkirta shi, musamman ma tunda yin sahur din yana da albarka, kada ka guje wa albarka; sai kuma gaggauta buda-baki da zarar rana ta fadi, saboda nunin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam), a kan haka.
Sannan mutum ya dage wajen yin sallar tarawiy a cikin jama’a, kada ya bari wani rudi ya dauke hankalinsa; ya kara yawaita karatun Alkur’ani yana tuntuntuni a kan ayoyinsa; ya yawaita sadaka da kyauta da kyawawan maganganu da dai duk ayyukan alheri, kuma kada ya gaza. Allah Ya taimake mu.
Nan za a kwana sai mako na gaba, lokacin da za a ga magana kan I’itikafi da zakkar fidda-kai da sallar idi, ina Allah Ya kai mu.
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!